Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 17 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 17 ga Watan Afrilu, 2019

1. Kotu ta umurci Hukumar DSS ta bayyanar da Sambo Dasuki

Kotun Koli da ke Maitama ta Abuja, babban birnin Tarayya, ta gabatar da wata umarni ga Hukumar DSS da cewa su tabbatar da bayyanar da tsohon shugaban hukumar bada shawarwari ga tsaron kasa (NSA), Sambo Dasuki.

Kotun ta gabatar ne da hakan a wata umarni da Alkali Husseini Baba-Yusuf ya bayar a ranar Talata da ya gabata da cewa Kotun na bukatar ganin Dansuki a gaban kotun kan wata kara da ake da shi.

2. INEC ta bada sabon sanarwa game da zaben kujerar sanatan Arewacin Jihar Imo

Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben kasar Najeriya, INEC ta bayyana da cewa hukumar ta kamala bincike da ta ke a kan wata zargin makirci akan zaben kujerar sanatan Arewacin Jihar Imo.

Hukumar ta gabatar da hakan ne a wata sanarwa da aka bayar ranar Talata da ta gabata daga bakin Mallam Mohammed Haruna, Kwamishanan Hukumar wajen Fasahan hidimar zaben.

3. Sabon Rikici a yayin da Hukumar EFCC ta sake kame Alkali Ofili-Ajumogobia

An yi wata sabon dirama a gaban Kotun Koli ta Ikeja a ranar Talata da ta gabata, a yayin da Hukumar Yaki da Cin hanci da Rashawa (EFCC) ta sake kame tsohon Alkalin Kotun Koli ta Tarayya, watau Alkali Rita Ofili-Ajumogobia, bayan da aka saketa kwanakin baya a kan wata zargin cin hanci da rashawa.

Naija News Hausa ta gane da cewa hukumar ta kame Malama Ofili-Ajumogobia a yayin da take kokarin fita daga cikin kotun missalin karfe 10 na safiyar ranar Talata, bayan lokacin da Alkali Hakeem Oshodi ya kamala gabatarwan sa.

4. Ma’aikata sun roki Buhari da rattaba hannu ga dokar kankanin albashin ma’aikata kamin ranar 1 ga watan Mayu

Ma’aikatan kasar Najeriya sun roki shugaba Muhammadu Buhari da cewa ya yi kokarin rattaba hannu ga takardan dokan biyan kankanin albashin ma’aikata na naira dubu 30,000 kamin ranar 1 ga watan Mayu da ke gabatowa.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gidan Majalisa ta mikar da takardan dokan biyar kankanin albashin ma’aikata na naira dubu 30,000 ga shugaba Buhari.

5. Nnamdi Kanu ya gabatar da sharidun da zai sa ya dakatar da yakin neman yancin Biafra

Shugaban ‘yan Kungiyar yaki da neman yancin Biafra, Nnamdi Kanu ya rantse da cewa zai dakatar da yakin neman yancin Biafra idan har shugaba Muhammadu Buhari zai iya bada kansa don gwajin jini da aka fi sani da DNA, don gane ko lallai Buhari da aka sani ne ke shugabancin kasar daga Aso Rock.

Naija News Hausa ta gane da wannan sabon bayanin Kanu ne a yayin da yake wata gabatarwa a gidan Radiyon Biafra a karshen mako da ta gabata.

6. Dalilin da ya sa muka sake kame Ofili-Ajumogobia – EFCC

Hukumar yaki da Cin hanci da Rashawa ta kasar Najeriya, EFCC ta gabatar da dalilin da ya sa suka sake kame tsohon alkalin kotun tarayya, Rita Ofili-Ajumogobia.

Hukumar ta gabatar da cewa sun sake kame Ofili-Ajumogobiata ne bisa wata mataki da hadin kan Kotun kara ta birnin Legas, a kan wata kara da ya shafi Alkali Hyeladzira Nganjiwa.

7. Nnamdi Kanu ya gabatar da takaitaccen hanyar da Atiku zai kada Buhari a Kotun Kara

Shugaban Kungiyar ‘yan Biafra, Mazi Nnamdi Kanu ya gabatar da wata takaitaccen hanyar da Atiku Abubakar, dan takaran kujerar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP a zaben 2019 zai iya bi don kada shugaba Muhammadu Buhari a karar da ake a Kotu kan zaben 2019.

Inji Kanu “Jam’iyyar PDP da Atiku su bukaci Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da yin gwajin jinin DNA don bada tabbacin cewa lallai shi ne ke akan shugabancin kasar”

8. Adeleke ya mayar da martani ga zargin da ake masa na bayar da takardan WAEC mara kyau ga INEC

Sanata da ke wakilcin Yamacin Jihar Osun daga Jam’iyyar PDP, Ademola Adeleke yayi watsi da zargin da ake a kansa na cewar ya bayyar da takardan WAEC mara kyau ne ga hukumar INEC a kan zaben Jihar Osun da aka kamala.

Naija News Hausa ta gane da cewa Kakakin yada yawu ga shugaba Muhammadu Buhari a hidimar yakin neman zabe, Festus Keyamo ne ya gabatar da zargin cewa takardan WAEC da Adeleke ya bayar ba mai kyau ba ne.

Ka samu kari da cikakken labaran Nejeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com