Uncategorized
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 18 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 18 ga Watan Afrilu, 2019
1. Majalisar Dattijai zasu gabatar da kasafin kudin shekara ta 2019 bayan Easter
Kwamitocin haɗin gwiwar gidan majalisan kasa a ranar Laraba da ta gabata sun gabatar da wata tsarin bil na kasa ta shekarar 2019 a gaban majalisar dattijai da majalisar wakilai.
Kwamitin sun bayar ne da bil din don ayi bincike da gabatar da amincewa akan haka.
2. Kadaria ta gabatar da barazanar yin Zanga-Zanga kan Kashe-Kashen da ake a Jihar Zamfara
Kwararra da Shahararar ‘yar watsa labaran kasan Najeriya, Kadaria Ahmed ta gabatar da barazanar cewa zata sake gudanar da zanga-zanga idan har ba a daina kashe-kashe ba a Jihar Zamfara.
Kadaria ta gabatar ne da hakan a wata gabatarwa da tayi a gidan Talabijin, ranar Laraba da ta wuce da cewa lallai tana da hakin yin hakan a matsayin ta na ‘yar kasa.
3. Wani Sanata a Jam’iyyar APC yayi murabus da kujerar sa akan wasu dalilai
Mista Benjamin Adanyi, daya daga cikin ‘yan Majalisa da aka dakatar daga shugabanci a Jihar Benue daga Jam’iyyar APC a yankin Makurdi, ya janye daga zaman dan majalisa.
Naija News Hausa ta gane da hakan ne a yayin da Adanyi ya gabatar da takardan dakatarwa ga magatakardan gidan majalisar a ranar Talata, 10 ga watan Afrilu ta shekarar 2019.
4. Gwamnatin Tarayya ta bayar da hutun Sallar Easter
Gwamnatin Tarayyar kasar Najeriya ta gabatar da ranar Jumm’a, 19 ga watan Afrilu zuwa ranar Litini 22 ga watan Afrilu a matsayin ranar hutu ga Ma’aikata don samun daman hidimar Sallar Easter ta shekarar 2019.
An gabatar da hakan ne a wata sanarwa da Gwamnatin Tarayya ta bayar daga bakin Sakataren Ayukan kasa, Georgina Ehuriah, wanda ya Wakilci Ministan Harkokin kasa, Lt.- Gen. Abdulrahman Dambazau, a ranar Laraba da ta gabata a birnin Abuja.
5. Gidan Majalisar Dattijai sun gabatar da Takardan Karfafa Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya
A ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu ta shekarar 2019 da ta gabata, Gidan Majalisar Dattijai sun gabatar da bil na karfa Hukumar Jami’an Tsaron ‘yan sandan Najeriya.
Naija News Hausa ta gane da cewa an gabatar da bil din ne don karfafa da kuma tabbatar da kyakyawar ci gaba ga hukumar ‘yan sandan kasar.
6. Kungiyar ‘yan Biafra na wata barazana da kalubalantar Shugaban Tsaro ga Buhari, Abba Kyari
Kungiyar ‘yan yakin neman yanci ga Biafra, IPOB na gabatar da wata zargi ga Abba Kyari, watau Shugaban Hidimar Tsaro ga shugaba Muhammadu Buhari, da cewa yana amfani da ‘yan sanda don cin mutuncin ‘yan kungiyar su.
Kungiyar IPOB sun gabatar da zargin ne a ranar Laraba da ta gabata.
7. John yayi watsi da matakin APC da gabatar da Gbajabiamila a matsayin dan takaran shugabancin Gidan Majalisar Wakilai
Mamban Gidan Majalisar Wakilai da ke wakilcin wata yanki a Jihar Benue, Hon. John Dyegh, ya gabatar da matakin sa na fita neman kujerar kakakin yada yawun gidan majalisar Wakilai ta tara.
Hon. John ya dauki wannan matakin ne bayan da Jam’iyyar APC ta gabatar da Femi Gbajabiamila, a matsayin zabin su ga kujerar.
8. Chibok: Majalisar Wakilai ta gayawa Gwamnatin Tarayya matakin da zata dauki akan Leah Sharibu
An gargadi Gwamnatin Tarayya da kara karfafa kokarin ribato yaran Leah Sharibu da sauran yaran Chibok da ‘yan ta’adda suka sace shekarun baya da suka gabata.
‘Yan Majalisar Wakilai ne suka gabatar da gargadin karfafawar ga shugabancin kasar.
Ka samu kari da cikakken labaran kasar Najeriya a shafin mu na Hausa.NaijaNews.Com