Connect with us

Uncategorized

‘Yan Sanda sun Kame Hassana da ta saka Guba cikin abincin Mijinta

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar ‘yan sandan Jihar Kano sun sanar da kame wata Macce da ta dauki matakin sa guba cikin abincin mijin ta.

Matar da ke da tsawon shekaru 15 ga haifuwa, Hassana Lawan daga kauyan Bechi da ke a karamar hukumar Kumbotso ta saka guba cikin abincin mijinta, Sale Abubakar da ke da shekaru 33 haifuwa.

Naija News Hausa ta gane da labarin ne a wata sanarwa da Kakakin Yada Yawun Hukumar ‘yan Sandan Jihar, DSP Abdullahi Haruna ya bayar.
DSP Abdullahi ya bayar ga manema labarai da cewa hukumar su ta karbi wata kirar gaugawa a ranar 16 ga watan Afrilu ta shekarar 2019, missalin karfe biyu na rana da cewa Hassana ta saka guba (maganin bera) a cikin abincin da Mijinta Sale ya ci.

“A halin yanzu Hukumar mu ta kai Malam Sale a asibitin Murtala Muhammad Specialist Hospital, da ke a birnin Kano, don samun cikakken bincike da kulawa” inji Abdullahi.

Ya karshe da cewa hukumar na kan bincike akan lamarin, kuma zasu dauki matakin da ya kamata ga Matar, musanman isar da ita Kotu bisa dokar kasa.

Idan akwai wata kari bayani akan wannan, zamu sanar a shafin labaran mu ta Hausa.NaijaNews.Com

Karanta wannan kuma: Gobarar wuta ya kame wani Makarantar Sakandiri a Jihar Kano