Connect with us

Uncategorized

Barayi sun kashe wani Mutum a Jigawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jami’an tsaron ‘yan Sandan Jihar Jigawa sun gabatar a ranar Alhamis da cewa wasu barayi sun kashe mutum guda da kuma yiwa wasu mugun raunuka a shiyar kauyan Garin Maidawa da ke a karamar hukumar Dutse ta Jihar Jigawa.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne a wata sanarwa da hukumar ta bayar daga bakin Kwamishanan tsaron Jihar,  Bala Zama, wanda ya bayar ga manema labarai a garin Dutse, da cewa barayin sun hari kauyan ne a missalin karfe Ukku na safiyar ranar Alhamis da ta wuce.

“Sun fada kauyan ne a lokacin da suka gane da cewa Jami’an tsaro basa kusa da shiyar. sun kuma gane da cewa kauye ne wajen” inji shi.

“Hukumar mu ma ba ta da Ofishi a wannan wajen. Wannan damar ne barayin suka yi amfani da ita don kai hari a kauyan, har ma da kashe mutum guda da kuma barin wasu jikin zafin raunuka”

“Sun hari gidan wani sannan matashi da ke a shiyar suka kashe sih, suka kuma yiwa kusan mutane biyar raunuka da bindiga da makamai,” inji Zama.

Ya bayyana da cewa ba a samu kame barayin ba amma an watsar da Jami’an tsaro a shiyar don neman kame wadanda suka aiwatar da mugun harin.

Bisa bayanin wani mazaunin shiyar, Malam Shamuddin Usaini, ya bayyana ga manema labarai da cewa barayin sun yi harin ne na kusan tsawon mintoci Arba’in da harbe harben mutane. inji Usaini a yayin da yake gabatarwa ga manema labarai a asibitin Rasheed Shekoni da ke a Jihar.

“Na gane da cewa sun fado kauyen ne da wata manufa. Da zarar isowan su, kwaram suka hari gidan Alhaji Liman, wani mai sayar da shanaye a garin” inji Usaini.

“Mun gano su ne a missalin karfe biyu na dare cikin kauyan da bindigogi da Sanduna” inji shi.

“Ba su bukaci komai ba daga kowa, amma dai sun tabbatar da harbin duk wanda ya leko da kokarin tarban su da hari”

Usaini ya bayyana da cewa kauyan bata taba samun irin wannan harin ba tun da take.