Connect with us

Uncategorized

Wata ‘Yar Makarantan Jami’a ta sha Guba don Soyayya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoton yadda wata ‘yar Makarantan Jami’a ta Jihar Kogi ta kashe kan ta da shan Gamale.

Yarinyar mai suna, Rebecca Michael ta kashe kanta ne da shan Gamale bayan da ta gane da cewa Masoyinta ya sake ta.

Da ganin hakan ne sai yarinyar cikin fusata ta sha gamale, da kuma dauke rayuwarta da kanta.

Abin takaici, an bayyana da cewa yarinyar ba ta dade da samun shiga Jami’ar ba, don tana karatun ta na shekarar farko a makarantar Jami’a ta Ayingba da ke Jihar Kogi, inda take karatun kwas na Philosophy a ‘Kogi State University’.

Bisa bayanin wani, ya gane da cewa Rebecca ba za ta wuce ‘yar shekara Ashirin (20) ba. Haka ta dauke rayuwarta da maganin Kwari wai don ta gane da cewa Saurayin ta da ke aikin DJ a Jihar ya bayyana da cewa bai sonta kuma.

Bisa ganewa da binciken Manema Labarai, an kai Rebecca a asibiti kamin ta mutu, amma ta kai ga karshen rai ne a yayin da ake bata kulawa a Asibitin FMC da ke a Lokoja.

Kakakin yada yawu Jami’an tsaron yankin, William Aya, ya bayyana da cewa bai karbi rahoto ba tukunna game da lamarin.

Ana kan bincike akan hakan, idan kuma akwai abin da ya biyo baya, zamu sanar a nan shafin Hausa.NaijaNews.Com

Karanta wannan kuma:Yan Sanda sun Kame Hassana da ta saka Guba cikin abincin Mijinta