Connect with us

Uncategorized

An kafa Dokar Daki Kulle na tsawon awowi 24 a Katsina-Ala don magance Hare-haren da ake kaiwa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin Jihar Benue ta sanar da dokan daki rufe don magance matsalar hare-hare da kashe-kashen da ke aukuwa a Jihar.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne bayan wata sanarwa da aka bayar ranar Litini da ta gabata da cewa wasu ‘yan hari sun sace Mutane biyar a garin, bisa bayan da aka kashe mutane goma sha daya a kauyan Ngibo, Tse-Aye ta yankin Ikyurav-Tiev 1, da ke a karamar hukumar Katsina-Ala a ranar Asabar da ta gabata.

An bayyana da cewa Mahara sun kuma gudu da Shanaye 28 na wani mutumi da aka sani da suna Barista Agwaza Atedze, a karshen makon da ta gabata, bayan da suka kara kashe kimanin mutane Hudu.

Harin bai tsaya a nan ba, a yayin da kuma ‘yan ta’adda suka haska wa gidajen mutane wuta a kauyukan ko ta ina. Mutanen kauyan kuma da suka gane da hakan sai suka yi gudun hijira da barin kayakin su don ceton rayuwar su.

Ganin hakan ne ya sa Gwamnatin Jihar ta kafa wannan dokar zama daki rufe har na tsawon awowi 24.

Engr. Benson Abounu, Gwamnan Jihar da ke kan shugabanci ne ya gabatar da wannan dokar daki rufe tun daga ranar Litini, 22 ga watan Afrilu, don magance matsalar tsaro da hare-hare da Jihar ke fuskanta.

Ya kuma gargadi Al’ummar yankunan da bin doka da umarnin da aka bayar don taimakawa Jami’an tsaro da tafiyar da aikin su a hanyar da ta dace.

“Duk wanda aka gane da rashin biyayya da wannan dokar, ko kuma da ke kokarin daukar wata mataki da zai karya dokar a wannan lokaci, lallai za a dauki mataki ta musanman akan wannan mutumin ko mutumiyar.” inji Benson.

Ya kuma bada tabbaci ga mutanen yankin da cewa an riga an samar da Jami’an tsaro a yankunan don magance matsalar tsaro a shiyar.

Bisa bayanin Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya ta ‘Operation Whirl Stroke’ (OPWS), Maj. Gen. Adeyemi Yekini, ya bayar da cewa kashe-kashen ya auku ne bayan wata farmaki da ta tashi tsakanin ‘Yan Shitile da kuma Ikyurav da ke a unguwar.