Connect with us

Uncategorized

Danjuma ya Kashe Matansa don tayi barazanar cewa Idan ya Mutu zata Sake Aure

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wani Mutumi mai shekaru Talatin da haifuwa da suna, Uwani Danjuma ya kashe matarsa don tayi barazanar cewa idan ya Mutu zata sake Aure.

Naija News Hausa ta gane da wannan rahoton ne da cewa Danjuma, wani mazaunin kauyan Uddu ta karamar Hukumar Rijau a Jihar Neja ya kashe matansa don ta bayyana zuciyar ta.

Bisa bayanin Danjuma, Ya ce “Matana ta mini barazana a lokacin da nike kwance da rashin lafiya da cewa zata Auri wani idan har na mutu.”

Da jin wadannan kalaman, sai Danjuma ya fusata, ya kuma kudura a zuciyarsa, bayan da ya samu saukin lafiyar jiki, sai ya hari matar da Adda, ya kashe ta.

Danjuma ya bayyana ga Jami’an tsaro da manema labarai da cewa lallai ya hari matan nasa ne a yayin da take cikin barci. Da cewa lallai ya kashe Matar ne akan fushin kalaman da ta furta.

“Banyi zaton cewa Matana zata iya furta kalaman nan ba, na cewar zata sake Aure idan har na mutu.” inji Danjuma.

“Haushin hakan ne ya kai ni ga daukar adda har na sassare ta a wuya da ya kai ta ga mutuwa. Banyi danasanin kashe ta ba tunda ita ma ta so ni ne da mutuwa, don ta sake aure. Ni kuma sai na kashe ta don ta rasa sake auren.” inji shi.

“Da ta sani da bata fadi hakan a kunne na ba. Ku bar ta taje ta shiga wuta da wannan kalaman nata”

Kakakin yada yawun Hukumar tsaron Jihar, Mohammad Abubakar, ya bayyana da cewa Jami’an tsaro sun kama Danjuma ne da zargin kisa, kuma za kai karar sa har ga kotu tun da ya tabbatar da kuma amince da zargin da ake da shi na kisa.