Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 23 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

 

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 23 ga Watan Afrilu, 2019

1. Gwamnatin Jihar Benue ta kafa dokar zama daki kulle na awowi 24 a yankin Katsina-Ala

Gwamnatin Jihar Benue a ranar Litini da ta gabata ta gabatar da dokar zama gida kulle har na tsawon awowi ashirin da Hudu a garin Katsina-Ala ta karamar hukumar Katsina-Ala.

Naija News ta gane da hakan ne bisa gabatarwa da aka bayar daga a ranar Litini da ta gabata a garin Makurdi, daga bakin Sakataren musanman ga Gwamnan Jihar, Mista Ede Ogaba.

2. Gidan Majalisa ba don cika gurin mutum daya bane, Saraki ya gayawa Tinubu

Shugaban Sanatocin Najeriya, Sanata Bukola Saraki ya mayar da martani game da zargin da ake a gareshi, musanman zargin da shugaban Jam’iyyar APC na Tarayya, Asiwaju Bola Tinubu ke yi da shi.

Dakta Sarakiya gargadi Asiwaju Tinubu da kafa kai ga zancen gaskiya da janye wa makirci.

3. Kotun Kara ta gabatar da sabon ranar karshe karar da ake akan zaben Jihar Osun

Kotun Koli ta birnin Tarayya ta Abuja ta gabatar da ranar 24 ga watan Afrilu 2019 don karshe karar hidimar zaben Jihar Osun bisa karar da Gwamnan Jihar, Adegboyega Oyetola da jam’iyyar sa APC suka gabatar a baya a gaban Kotu.

Naija News Hausa ta tuna da cewa Gwamnan da Jam’iyyar APC sun gabatar da karar ne akan sakamakon zabe da aka gabatar a Jihar na zaben 2019 a ranar 22 ga watan Maris da ta gabata.

Information about the hearing date is contained in notices sent to parties by the court’s Registry.

4. IPOB: Asari Dokubo ya bayyana wadanda suka kashe Annabi Nwoko

Tsohon shugaban kungiyar ta’addancin yankin Niger Delta, Asari Dokubo, ya zargi shugaban kungiyar ‘yan iyamirai da ke yaki da yancin Biafra, Nnamdi Kanu, da kisan Annabi Anthony Nwoko.

Shafin Naija News ta turanci ta ruwaito a wata sanarwa a baya da cewa wasu ‘yan ta’adda da ba a gane da su ba, sun kashe Annabi Nwoko a gidan sa da ke shiyar Enugu.

5. Shugabancin Buhari ya kasa ga cika bukatar ‘yan Najeriya – inji Jam’iyyar PDP

Jam’iyyar Adawa, PDP ta gabatar da sabuwar zargi a ranar Lahadi da ta gabata da cewa shugabancin Muhammadu Buhari ta kasa ga cika guri da kuma biyan bukatar ‘yan Najeriya gaba daya.

PDP sun kara da cewa Ministocin kasar da Hukumomi basu ci wata sabuwar nasara ko kawo ci gaba a kasar ba cikin shugabancin su na tsawon shekaru hudu da suke a mulki.

6. Gwamna Bello ya bayyana dalilin da ya sa ba zai iya aiki tare da Dino Melaye ba a Jihar Kogi

Gwamnan Jiahr Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya bayyana dalilin da ya sa shi da Sanata Dino Melaye ba zasu iya aiki tare ba a Jihar Kogi.

Yahaya ya kara da cewa, a gaskiya shi da Dino ba zasu iya hada hannu da aikin Jihar ba don gurin su ga Jihar ba daya ba ne.

7. Dakatarwan Onnoghen ya kasance ne akan makircin Zabe  – Tanko Yakasai

Babban Tsoho da Mai Fadi a Ji a Jiha, Tanko Yakasai ya yi Izgilin matakin Kotun Kara akan dakatar da tsohon babban shugaban alkalan kasar Najeriya, Alkali Walter Onnoghen.

Naija News Hausa ta gane da zargin ne a wata gabatarwa da aka bayar a ranar Lahadi da ta gabata, a bakin Yakasai.

 

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com

Advertisement
close button