Connect with us

Uncategorized

‘Yan Sandan Jihar Katsina sun gabatar da kashe ‘yan ta’adda fiye da 9, a Lahadin da ta gabata

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Litini da ta gabata, Hukumar tsaron ‘Yan Sandan Jihar Katsina sun gabatar da barazanar cewa sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 9 a kauyan Sherere da ke a karamar Hukumar Kankara.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne a wata gabatarwa da aka bayar daga bakin Kakakin yada yawun Jami’an tsaron Jihar, SP Gambo Isah, wanda ya bada tabbacin hakan da cewa Hukumar su a ranar Lahadi da ta wuce sun kashe ‘yan ta’adda fiye da tara a kauyan Sherere.

An bayyana ne da cewa Maharan sun fada a kauyan ne da harbe-harbe ko ta ina bayan shigar su a kauyan akan Babura.

Bisa bayanin wani wakili daga kauyan, Dikko Sherere, ya bayar ga manema labarai da cewa kimanin mutane goma ne aka kashe a harin.

Amma bisa fadin kakakin yada yawun ‘yan sandan Jihar, Ya ce “Lallai akwai tabbacin harin, amma dai  ba mutane goma bane aka kashe, mutane 9 ne. Inji Shi.”

Ya kara da cewa an riga an watsar da rukunin Jami”an tsaro ta ‘Operation Puff Adder’ don yaki da kuma ganin cewa sun gabo ko suwaye suka aiwatar da kashe-kashen.

“Hukumar mu na gargadi da rokon al’ummar yankinan nan da taimaka da duk wata liki da zai iya kai ga saukin kamun ‘yan ta’addan.” inji shi.

Ya kuma gabatar da gaisuwa da sakon gaisuwa da jinya ta musanman ga Iyalan mutanen da aka kashe.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa da cewa Hukumar Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan Jihar Jigawa sun sanar da gane wani dan Jariri da Maman tayi watsi da shi bayan haifuwa.

Bisa bayanin Jami’an tsaro, an ajiye jaririn ne a cikin wata rijiya da ba a amfani da shi, da ke a wata shiyya na karamar hukumar Kaugama.