Connect with us

Uncategorized

Kash! An yanka ta tashi, An daga ranar Auren Adam A. Zango da Softy

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Adam A Zango, Naija News Hausa, Labaran Hausa, Softy, Hausa News, Kannywood, Latest Hausa News, Labaran Arewa

Adam A. Zango, Shahararren dan shirin fim a Kannywood ya gabatar da daga ranar Auren sa bisa wasu dalilai.

Naija News Hausa ta gane bisa wata sanarwa da cewa ya kama ayi hidimar Auren Adam ne a wannan karshen Makon, amma sai abin ta kasance ‘An yanka ta tashi’.

Adam da kansa ya wallafa wata sabuwar sakon sanarwa ga dukan masoya da cewa lallai an daga ranar Auren na sa da Softy har sai zuwa bayan Sallah.

“Salam ‘Yan Uwa da Abokannan Arziki. An daga Aure na zuwa bayan Salla. Zan sanar maku da sabon lokacin da aka tsayar” inji Adam a cikin sakon sa.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Adam A. Zango ya nemi Sulhu da Ali Nuhu