Connect with us

Uncategorized

Kimanin Mutane 19 sun rasa rayukansu a wata Hadarin Mota a Jihar Jigawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kimanin mutane Goma-Shatara suka rasa rayukan su a wata hadarin Motar Bus da ya faru a wata shiya ta karamar hukumar Gwaram, a Jihar Jigawa.

A ranar 23 ga watan Afrilu 2019, watau ranar Talata da ta wuce, anyi wata hadarin mota da ya dauke yawar rayuka kusan 19. Mutanen sun kone kurmus da gobarar wuta a yayin da hadarin ya faru.
An bayyana da cewa wasu kuma sun yi raunuka hade da wani karamin yaro da shi ma ya samu rauni.

Bisa bayanin wani, ya bayyana da cewa Maman Yaron ta jefar da shi ne ta tagar motar a yayin da ta gane da hadarin.

Wani da ya samu ganin yadda hadarin ya faru, ya bayyana da cewa Motar Bas din mai lamba KTG245YG, ta fito ne daga hanyar Katagum daga garin Bauchi zuwa garin Ningi.

Ya kara da cewa Motar na dauke da mutane cikke ne a ciki zuwa wata bikin Aure.

Ya ce “Motar ta yi hadarin ne a yayin da tayar gaba ya fita wuf, sai motar ta dinga juyawa da su daga nan ta kame da wuta a baya”

Ko da shike ba cikakken bayani a lokacin da aka karbi wannan rahoton, amma kakakin yada yawun Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Jihar, Abdu Jinjiri ya bada tabbacin hadarin.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa wasu ‘yan Makarantan Kwalejin ‘Sokoto State College of Education’ hade da wasu mutane biyar sun rasa rayukan su a wata hadarin mota da ya faru a hanyar da ta bi Maiyama zuwa Jega, a Jihar Kebbi.

Bisa ga bayanin wani da ya gana da hadarin, Ya bayyana da cewa Motar Toyota Tercel da ke dauke da ‘yan makarantan daga garin Kotongora, Jihar Neja ya hade ne da wata Tirela a yayin da suka kusanci Maiyama, wata gari da ke a Jihar Kebbi.