Connect with us

Labaran Najeriya

Zamu canza rawar mu idan har Gwamnatin Tarayya ta ki sakin Sheik El-Zakzaky -IMN

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kungiyar Ci gaban Addinin Musulunci ta Najeriya (IMN) da aka fi sani da ‘Yan Shi’a sun gargadi Gwamnatin Tarayya da cewa kada su kara jinkiri ko kuma kaisu ga fusata akan rashin sake shugaban kungiyar su, Sheik Ibrahim El-Zakzaky.

Kungiyar ta gabatar da gargadin ne ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya a ranar Talata da ta gabata, a yayin da suke taya El-Zakzaky murna na kai ga shekaru 68 da haifuwa, da kuma bacin ran cewa shugaban ya kai ga tsawon kwanaki 1,224 a kulle nan cikin birnin Abuja.

A bayanin shugaban kungiyar ‘yan Shi’a ta Jihar Sokoto, Sheikh Sidi Munnir, da manema labarai, yayi barazanar cewa kungiyar zata dauki sabon salo idan har Gwamnatin Tarayya ta ki sakin shugaban su.

Da aka tambaye shi akan matakin da kungiyar zata dauka idan har Gwmanatin Tarayya ta ki sakin El-Zakzaky, sai ya ce “Lallai idan har Gwamnatin Tarayya ta ki sakin shugaban mu, ba wannan zanga-zanga zamu ci gaba da yi ba, zamu canza rawarmu.” inji Sheikh Sidi.

“Amma dai ina zato da tunanin cewa shugaba Muhammadu Buhari zai dauki matakin a wannan lokacin na sakin shugaban mu. Amma idan hakan bai samu ba, dole ne mu canza takan rawar mu.”

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Kungiyar Zamantakewa ta Musulumman Najeriya (IMN), da aka fi sani da suna ‘Yan Shi’a sun fada da cewa basu da goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari ga zaben 2019.