Connect with us

Labaran Najeriya

Ziyarar Buhari: Shugaba Muhammadu Buhari ya isa Jihar Legas a Yau

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Laraba, 24 ga watan Afrilu 2019, Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci birnin Legas don wata kadamarwa

Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci Jihar Legas a yau don kadamar budewar Manyan hanya mai taki Goma ta Oshodi zuwa Babban Filin Jirgin Murtala Muhammed da kuma kadamar da wata Asibiti ta Ayinke House (Maternity Hospital) da ke a Makarantar Jami’an Koyar da Kiwon Lafiya ta Ikeja, da dai sauran su.

A yayin da shugaba Buhari ke sauka a Jirgin Sama, ya samu marabta daga Gwamnan Jihar Legas, Gwamna Akinwunmi Ambode da wasu Gwamnonin kamar, Gwamnan Jihar Ogun, Ibikunle Amosun, Gwamnan Jihar Oyo,  Abiola Ajimobi da kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi.

Haka kazalika shugaban ya karbi marabtan sabon Gwamnan Jihar Legas bisa zaben 2019, Babajide Sanwo-Olu da mataimakin sa Obafemi Hamzat, da dai wasu da ba a bayyana sunayan su ba.

Naija News Hausa ta tuna da cewa shugaba Muhammadu Buhari a ‘yan kwanaki da ta wuce ya rattaba hannu ga takardan dokan biyan kankanin albashin ma’aikatan kasa ta naira dubu Talatin, N30,000.