Connect with us

Labaran Najeriya

An bada Hutu ga Ma’aikatan Jihar Borno don Marabtan Shugaba Buhari

Published

on

Gwamnatin Jihar Borno ta gabatar da Hutu a yau Alhamis, 25 ga Watan Afrilu ga ma’aikata da ‘yan makaranta don fita marabtan shugaba Muhammadu Buhari ga ziyarar sa a Jihar.

An gabatar da wannan sanarwan ne daga bakin Kwamishanan Yada Labarai, Dakta Mohammed Bulama

A bayanin Dakta Bulama a ranar Laraba da ta gabata, ya ce “Saboda ziyarar shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a Jihar Borno, Gwamnatin Jihar Borno na sanar maku da hutu ga ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu 2019, don samun fita marabtan shugaba Buhari.”

“Gwamnatin Jihar na roko da duk wata matsalar barnan lokaci ko tsari ga duk wani ko wata a wannan ziyarar. Muna kuma gargadin kowa da fitowa don marabtan shugaban kasar.” inji shi.

Karanta wannan kuma: Kungiyar Sarakunan Jihar Katsina ta Tsige Hakimai biyu daga wakilcin yankunan su.