Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 25 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 25 ga Watan Afrilu, 2019

1. ‘Yan Shi’a sun fada Gidan Majalisa da Zanga-Zanga

Wasu mambobin Kungiyar Cin Gaba ta Musuluncin Najeriya da aka fi sani da ‘Yan Shi’a’ sun fada ga Gidan Majalisar Dattijai da Zan-Zanga da har sun sa dole Majalisa ta daga zamar su zuwa gaba.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa ‘Yan Shi’a sun yi barazanar daukan sabon mataki idan har Gwamnatin Tarayya ta ki sakin shugaban Kungiyar su.

2. Zaben Jihar Osun: Wasu rukuni na zargin Tinubu da kokarin kaurace wa Shari’a Kotun Kara

Wata Hukumar Yaki da Yancin Al’umman Kasa ta daga murya da gane da shirin shugaban Jam’iyyar APC na Tarayya, Bola Tinubu, akan wata shirin Kaurace wa matakin Kotun Kara game da zaben Jihar.

Naija News Hausa ta tuna a baya da cewa Kotun Kara ta gabatar ne da Sanata Ademola Adeleke a matsayin mai nasara ga zaben Jihar Osun a zaben da aka kamala a baya.

3. Ruduwa a Gidan Majalisa akan wanda zai shugabancin Majalisar Wakilan Kasar

Kakakin yada yawun Gidan Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da Darukan sa na cikin ruduwa akan wanda za a zaba a matsayin sabon shugaban Gidan Majalisar.

Naija News Hausa ta gane da cewa Jam’iyyar APC sun riga sun bayar da Femi Gbajabiamila a matsayin dan takaran su ga kujerar shugabancin gidan majalisar.

4. Gidan Majalisar Dattijai sun daga hidimar gabatar da kasafin kasa ta shekarar 2019

A ranar Laraba da ta gabata, Gidan Majalisar Dattijai sun dakatar da hidimar gabatar da kasafin kudin kasa ta shekarar 2019 zuwa mako ta gaba.

Ka tuna a baya da cewa Gidan Majalisar ta bayar da cewa zasu gabatar da kasafin kudin ta shekarar 2019 a ranar Laraba da ta gabata.

5. Yadda Obasanjo ke da alhakin Matsalar da Najeriya ke fuskanta a yau – Femi Falana

Mista Femi Falana a ranar Laraba da ta wuce, ya bayyanar da wata dalilin da ya sa tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ke da alhaki ga matsalolin da kasa ke ciki.

“Ya kamata kasar Najeriya ta cinma nasara ga matsalolin da take fuskanta, Idan da ace Obasanjo bai hana shugabanci daga karamar hukumar gidan Majalisar ba.” inji Falana.

6. Wani Lauya ya gabatar da Kara a Gidan Majalisa Buhari da Gwamnatin kan Tanko Muhammad.

Alkali Malcom Omirhobo, ya gabatar da sabuwar kara a Kotun Koli ta Abuja akan sanya Alkali Tanko Muhammad a matsayin shugaban Alkalan kasar.

Naija News Hausa ta tuna a baya da cewa an Tsige Alkali Walter Onnoghen  daga kujerar shugabancin Alkalan Najeriya, aka kuma sanya Tako Muhammad a maimakonsa.

7. An gabatar da Hutu a Jihar Borno don marabtan shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamnatin Jihar Borno ta gabatar da Hutu ga ma’aikata da ‘yan makaranta don fita marabtan shugaba Muhammadu Buhari ga ziyarar sa a Jihar.

An gabatar da wannan sanarwa ne daga bakin Kwamishanan Yada Labarai, Dakta Mohammed Bulama

8. Muna da Isassun Daktoci a kasar Najeriya – inji Ngige

Ministan Aikace-aikace, Dakta Chris Ngige ya gabatar da cewa kasar Najeriya na da albarkacin Daktoci da yawar gaske, kuma duk daktoci masu zuwa kasashen waje don aiki basu raunana kasar Najeriya ba.

“Kasar Najeriya na da Daktoci da yawar gaske, duk wani dakta da ke da muradin tafiya zuwa kasar waje yana da damar haka, bai raunana kasar mu ba ko ta yaya.” inji Ngige.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com