'Yan Shi'a sun yiwa Ofishin Gidan Majalisar Dattijai barna | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labarai Hausa

‘Yan Shi’a sun yiwa Ofishin Gidan Majalisar Dattijai barna

Published

Mun ruwaito a baya a Naija New Hausa, a wata sanarwa da cewa kungiyar ‘Yan Shi’a sun fada wa Ofishin gidan Majalisar Dattijai da Zanga-Zanga da bukatar Gwamnatin Tarayya da su saki Sheik Ibrahim El-Zakzaky, shugaban kungiyar su.

A halin yanzu, Naija News ta samu rahoto da cewa Gidan Majalisar ta sanya masu gyara a kofar shiga Ofishin don gyara barnan da kungiyar IMN (Yan Shi’a) suka yi a lokacin da suka hari Ofishin da zanga-zanga a ranar Laraba da ta gabata.

An gano ma’aikata masu gyaran kofofi da karfuna a gaban Ofishin a yau a yayin da suke gyara gaban Ofishin.

Ka tuna da cewa Kungiyar ‘Yan Shi’a sun yi barazana a baya da cewa zasu canza rawar su idan har Gwamnatin Tarayya ta ki sakin Sheik Ibrahim El-Zakzaky daga kulle.

Karanta wannan kuma; Wani Mutumi mai shekaru Talatin da haifuwa da suna, Uwani Danjuma ya kashe matan shi don tayi barazanar cewa zata sake Aure idan ya Mutu.

 
Kuna iya aika Naija News ta hanyar amfani da maɓallin rabar mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa [email protected].