Connect with us

Labaran Najeriya

Idan ma kun ce Buhari yaje binciken lafiyar jikin sa ne, ba gardama – inji Femi Adesina

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mataimakin shugaba Muhammadu Buhari ta hanyar yadarwa da sanarwa, Mista Femi Adesina yayi bayani game da ziyarar kai tsaye da shugaban yayi zuwa kasar UK, kamar yadda Naija News Hausa ta sanar a baya.

“Kowa na da damar furta zucciyar sa da kuma yada yawun sa ga duk abinda ya gadama. Idan ma ance Buhari ya je bincike lafiyar jikin sa ne, ba gardama.” inji Femi.

Mista Adesina yayi wannan bayanin ne don mayar da martani game da jita-jitan da ‘yan Najeriya ke yi na cewar shugaba Muhammadu Buhari yayi tafiya ne zuwa kasar UK don binciken lafiyar jikin sa.

“Duk masu muradin yada yawun su, suna da damar haka, duk masu jita-jita suna iya ci gaba da hakan. Idan mutum yayi tafiyar kai tsaye zuwa ko ina, lallai mutumin na da damar yayi duk abinda ya gadama a tafiyarsa.”

Wannan itace bayanin Femi Adesina a wata zaman tattaunawa da yayi a gidan Talabijin da ake cewa ‘Channels Television’, a ranar yau Jumma’a, 26 ga watan Afrilu ta shekarar 2019.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa matan shugaban kasar Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari ba ta samu damar yawon hidimar yakin neman zabe da maigidan ta ba a watan Janairu da ta gabata. An bayyana a lokacin da cewa Aisha tayi tafiya zuwa Turai ne don kulawa da lafiyar jikin ta.

Ko da shike ba a bayyana ko menene sanadiyar rashin lafiyar Aisha Buhari ba a lokacin, ba wanda kuma ke da sanin irin cuta ko illar jiki da ke damunta. Amma dai an gabatar da cewa kawai bata da lafiya kuma ta je Turai don kulawa da jikin na ta.