Uncategorized
Rana ta baci! An kame wani Barawo da ke kokarin Sace Mota a Nyanya
Hukumar Jami’an tsaron kasa, ‘Yan Sanda sun ceci ran wani da ake zargi da sace wata mota
Jami’an ‘Yan sandan Najeriya ta rukunin Birnin Tarayya, Abuja, sun ceto ran wani mutumi mai suna Yakubu Mohammed daga hannun ‘yan shiyar Nyanya da suka yi kokarin kashe shi.
Naija News Hausa ta gane da cewa an kame mutumin mai shekaru 40 da haifuwa ne a yayin da yake kokarin sace wata mota a ranar Asabar da ta gabata.
Da mutanen unguwar suka gane da shi sai aka hau shi da bugu har da kokarin kashe shi a nan. Suna cikin hakan ne sai Ofisoshin ‘yan sandan yankin Nyanya suka hallaro wajen don ceton ran sa daga mutuwa a lokacin.
An bayyana da cewa mutumin, Mohammed ya saba sace motocin mutane da ire-iren makullai da yake tsarrafowa da kanshi.
Sabon Kakakin Jami’an tsaron yankin FCT, birnin Tarayya, Mista Gajere Danjuma ya badda tabbacin hakan da cewa lallai an ceto ran Mohammed kuma ‘yan sanda sun kame shi nan take.
Ya kuma bayyana da cewa sun iya gano Mohammed da makullin motar Toyota da wasu makullai kuma a lokacin da aka kame shi.
Mohammed mutumin Ankpa ne a Jihar Kogi, Ya kuma fada hannun kamu ne a ziyarar sa zuwa birnin Abuja wajen ‘Yar Uwan shi, inda ya yi kokarin sace mota a unguwar.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa wasu ‘Yan tada zama tsaye a Jihar Legas sun yi wa wani Sojan Najeriya mugun duuka a yayin da yake kokarin ‘kare su daga kashe wani direban babban mota da bugu.