Connect with us

Labaran Najeriya

Bai dace Mataimakin Shugaban Kasa ya dauki gurbin shugabanci ba idan shugaba ya Mutu – inji Sheikh Sani Jingir

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Idan Shugaban Kasa ya mutu akan mulki, bai kamata mataimakin sa ya ci gaba da mulki ba

Wani Malamin Arabi mai suna, Sheikh Sani Yahaya Jingir yayi kira ga Gwamnatin kasar Najeriya da sake diba da gyara dokar kasar, musanman hana duk wani mataimakin shugaban kasa da ci gaba da maye gurbin shugaban idan har ya mutu a kan shugabanci.

Sheikh Jingir ya gabatar ne da wannan bayanin a ranar Lahadi da ta gabata, a wata gabatarwa da yayi ga hidimar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah (JIBWIS’s) ta Ashirin da Shidda (26th national annual seminar) a garin Jos.

“A gani da ganewa na, bai dace ba ace wanda al’ummar kasar Najeriya basu zabe shi ba ya maye gurbin shugabancin kasar bayan da shugaban kasar ya mutu.” inji Sheikh Jingir.

“Dokar kasar Najeriya ta bada dama ne kawai ga zaben shugaban kasa a lokacin hidimar zabe, ba kuwa mataimakin shugaban kasa ba. Saboda hakan ban ga dalilin da zai sa mataimakin shugaban kasa zai maye gurbin shugabancin kasar ba idan shugaban sa ya mutu akan mulki.”

Sheikh Sani Jingir ya kara da cewa “Idan akwai wani mataimakin shugaban kasa da ke bukatar hakan, ya kamata ya bayyana kansa a kuma zabe shi lokacin hidimar zaben kasar.”

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana murnan sa da irin mataimaki, abokin takara da ya ke da shi, watau hadewar sa da Farfesa Yemi Osinbajo.

Wannan itace bayanin shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da Farfesa Yemi Osibanjo yayi wata hadarin jirgin Sama a Jihar Kogi a kwanakin baya.

“Na Gode wa Allah da kare mataimaki na, Farfesa Yemi Osibanjo daga hadarin jirgin sama da ya yi” in ji Buhari.

“Ina yaba wa mataimaki na da kuzari, kokari da kuma irin karfin lamirin zuciya da ya ke da shi, harma da iya ci gaba da hidimar yakin neman zaben bayan hadarin da ya faru da shi a ranar”

Bayanin shugaba Muhammadu Buhari ke nan a ranar Lahadi, 3 ga Watan Fabrairun 2019 da ta gabata, kamar yadda aka bayar daga bakin Kakin yada yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a birnin Abuja.