Connect with us

Uncategorized

Boko Haram sun kashe Sojoji 5, Talatin kuma sun bata a Jihar Borno

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kimanin Sojojin Najeriya biyar suka rasa rayukan su a wata sabuwar ganawar wuta da ‘yan Boko Haram a Jihar Borno.

Naija News Hausa ta karbi rahoto a yau Litini da cewa Rundunar Sojojin kasa ta Najeriya sun yi wata ganawar wuta da ‘yan ta’adda a ranar Jumma’a da ta gabata, inda ‘yan ta’addan Boko Haram suka samu cin nasara da kashe sojoji biyar daga cikin sojojin Najeriya a nan take.

Bisa bayanin wani da bai bayar da sunan sa ba ga manema labarai, ya gabatar da cewa Rundunar Sojojin kasar sun samu gano da gawakin sojoji biyar da aka kashe. “An gano gawakin Sojoji biyar da suka mutu amma har yanzu ba a samu ganin kimanin sojoji Talatin ba da suka halarci ganawar wutan”

Ya kara da cewa har wa yau Rundunar sojojin na cikin bincike da neman sojoji kimanin 30 da suka bata a harin wanda ba wanda ya san inda suke, inji shi.

Naija News Hausa ta samu sanin cewa ‘yan ta’addan da aka fi sanin sunar kungiyan su da ‘ISWAP’ ne suka hari rukunin Rundunar Sojojin kasa ta Najeriya a ranar Jumma’a da ta wuce a rukunin su da ke a shiyar Mararrabar Kimba, mai Kilomita 135 daga garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Mun ruwaito a baya a shafin Labaran Hausa ta gidan yada labaran mu, da cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa Dokar ƙuntatawa na tsawon awowi 24 a Jihar.

An gabatar ne da dokar ƙuntatawa a ranar 26 ga watan Afrilu ta shekarar 2019 a layin yanar gizon nishadarwa ta Facebook, kamar yadda Samuel Aruwan, Kakakin yada yawun Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya rabar.