Connect with us

Uncategorized

Gobarar Wuta ya kame wata Tiransifoma a birnin Abuja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Gobarar Wuta, Naija News Hausa, Hausa News, Labaran Hausa, Labaran Najeriya a yau

Naija News Hausa na sanar da wata gobarar wuta da ta auku a birnin Abuja, ranar Lahadi da ta gabata.

Bisa bincike da yadda aka bayar a rahoto, abin ya faru ne a shiyar Apo, inda wata Tiransifomar wutar Lantarki ta dauke da gobarar wuta a missalin karfe daya da rabi (1:30PM) ta ranar Lahadi, 28 ga watan Afrilu da ya wuce a nan Abuja, babban birnin Tarayyar kasar Najeriya.

Hukumar samar da wutan lantarki ta Najeriya sun gabatar da bada tabbacin hakan da cewa lallai tiransifoma da ke a shiyar Apo mai girman lamba kamar haka 45MVA 132/33kV ta kame da gobara.

An gabatar da cewa an ci nasara da kashe gobarar wutan ne tare da hadin kan birnin Tarayyar da kuma hukumar yaki da gobarar wutan Kamfanin Man Fetur.

“Ko da shike babu tabbacin cewa watakila za a samu gyara tiransifomar, sai har hukumar TCN ta bada tabbacin hakan.” inji Manajan TCN, Ndidi Mbah.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa gobarar wuta da ya kone Shaguna Shidda (6) a Birnin Kebbi ranar Jumma’a da ta gabata.

Daya daga cikin masu gadin kasuwar, Malam Aminu Shehu, ya bayar ga manema labarai da cewa har yanzu ba su iya sun gane da sanadiyar kamun wutar ba. Amma da cewa Hukumar Yaki da Gobarar Wuta (Fire Service) ne suka taimaka da kashe yaduwar wutan cikin kasuwar.