Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 29 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Published

on

at

advertisement

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 29 ga Watan Afrilu, 2019

1. Zan tabbatar da karban Yanci Na, Atiku ya gayawa Magoya bayansa

Dan takaran kujerar shugaban kasa daga jam’iyar PDP ga zaben 2019, Atiku Abubakar ya gabatar ga mabiya bayansa da cewa lallai zai tabbatar da karban yancin sa da aka kwace.

Atiku ya gabatar da hakan ne a wata gabatarwa ta karfafawa ga Masoyan ATIKULATED duka da ya wallafa.

2. Biafra: Nnamdi Kanu ya samu marabta daga taron mutane mai yawa a birnin Jameni

Shugaban Kungiyar yaki da yancin ‘yan Biafra (IPOB), Nnamadi Kanu ya samu girmamawa da marabta ta musanman daga masoya da mabiya a garin Bavaria Munich, ta kasar Jameni.

Naija News ta ruwaito a wata sanarwa a baya da cewa Nnamdi Kanu ya sanar da cewa zai yi wata gabatarwa a ranar 24 ga watan Afrilu a birnin Jameni.

3. An bukaci Buhari da kalubalantar matsayin da aka nada diyar Abba Kyari

Wata kungiyar Yancin Al’umma ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da daukar matakin gaugawa na kalubalantar matsayin da aka nada Malama Aisha Abba Kyari, watau matsayin mataimakiya ga shugaban kungiyar NSIA).

Hukumar Bincike akan Makirci da Cin Hancin shugabancin kasa (CACOBAG), ta gabatar da cewa wannan zabin da aka yi ga Aisha na da alamun jawo gwagwarmaya da matsala.

4. Rikici a rukunin PDP akan zabin Lawan, Goje da Ndume game da shugabancin Gidan Majalisai

Rukunin Jam’iyar PDP na cikin ruduwa da rikici a yayin da suke kacici-kacici akan wanda zai wakilci Jam’iyyar ga takaran shugabancin Gidan Majalisar Dattijai da ta Wakilai.

Naija News ta gane da cewa Jam’iyyar PDP na hakan ne don tsayar da dan takara da zai yi jayayya da ‘yan takaran Jam’iyyar APC ga kujerar Gidan Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai.

5. Ban raunana ko ji haushin nasarar Balogun ba ga kujerar Sanatan Jihar Oyo
Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi yayi bayanin cewa bai raunana ba ko kuma ji dabam ba ga kayar dashi ga zabe da dan takaran kujerar Sanatan Jihar, Dakta Kola Balogun daga Jam’iyyar PDP yayi.

Yayi wannan bayanin ne a wata ganawa ta hidimar wasannin gargajiya da nishadarwa da aka yi a birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

6. Rundunar Sojojin sun bada tabbacin sabon nasara da ‘yan ta’adda a Jihar Zamfara

Rukunin Operation Sharan Daji ta rundunar Sojojin Najeriya ta gabatar da kashe ‘yan ta’adda hudu a Jihar Zamfara a wata ganawar wuta ta karshen mako da ta gabata.

Naija News ta samu sanin cewa ‘yan ta’addan sun ci nasara da yiwa sojojin Najeriya 6 raunuka.

7. Shugaba Buhari ya kafa kai ga zancen Shugabancin Gidan Majalisai

Shugaban Muhammadu Buhari ya shiga zancen shugabancin gidan Majalisar Dattijai da ta Majalisar Wakilai. ya kuma nuna zabin sa ga sanya Dakta Ahmed Lawan a matsayin shugan gidan Majalisar Dattijai, sa’anan kuma Mista Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban gidan Majalisar Wakilai.

Shugaban yayi hakan ne don magance matsalar da aka samu a shekarar 2015 ga zaben shugabancin gidan Majalisai ta 8.

8. Shugabancin kasa ta kadamar da bincike akan masu Kire-kire a Jihar Zamfara

Shugabancin kasar Najeriya ta kafa kai da bincike jerin sunayan wadanda aka bayar da dama don aikin ma’adinai a Jihar Katsina.

An yi hakan ne don magance matsalar ta’addancin da hare-hare da ake yi a Jihar Zamfara.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com