Connect with us

Labaran Najeriya

An bada Hutun Ranar Ma’aikata na 1 ga Watan Mayu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Hutun Ranar Ma'aikatan Kasar Najeriya, Labaran Najeriya a Yau, Naija News Hausa,

Gwamnatin Tarayyar kasar Najeriya ta Gabatar da ranar Laraba, 1 ga watan Mayu a matsayin ranar Hutu don bikin Ranar Ma’aikatan Kasa ta shekarar 2019.

Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne bisa sanarwa da Gwamnatin Tarayya ta bayar daga bakin Ministan Harkokin Kasa, Lt.- Janar (Rted) Abdulrahman Dambazau.

Janar Dambazau ya gabatar da hutun a wata sanarwa da yayi a wakilcin Gwamnatin Tarayya, inda ya jinjina wa sadaukarwan Ma’aikatan kasar musanman da irin Gwagwarmaya da kokari da suke wajen gina kasar.

Wannan shi ne bayanin Dambazau a sanarwan da aka bayar a ranar Litini da ta gabata a birnin Abuja, daga bakin Malama Georgina Ehuriah, sakataren musanman ga Ministan Harkokin kasar.

Dambazau ya kara a cikin bayanin sa da karfafa Ma’aikatan kasar Najeriya musanman ga kokarin karfafa da gyara Tattalin Arzikin kasar Najeriya zuwa gaba.

Ya kuma jinjina masu da irin bada kai da suke yi ga shugabancin Muhammadu Buhari wajen samar da ci gaba a kasar Najeriya.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Buhari ya Rattaba hannu ga biyan Kankanin Albashin Ma’aikata na naira 30,000.

Wannan ya biyo ne bayan da Gidan Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai suka amince da dokar da kuma sanya hannun su a kwanakin baya.