Connect with us

Uncategorized

Kalli bayanin Dan kwallon kafa na Liverpool game da wasar su da Barcelona a gobe

Published

on

at

Labaran Wasan Kwallon Kafa, Naija News Hausa, Labaran Wasannai, Kwallon Kafa, Wasan Champion League
advertisement

Dan wasan Kwallon kafa na Liverpool, Virgil van Dijk ya bayyana da cewa bai raunana a zuciyarsa ba akan hadewar su da ‘yan kwallon Barcelona a gobe ba.

“Bani da wata raunin zuciya ko tsoro akan ganawar mu da kungiyar kwallon Barcelona a gobe, musanman yadda zamu hana shaharraren dan kwallon duniya, Lionel Messi daga yin motsi a wasar mu da su a Champions League” inji Virgil.

Naija News Hausa na da sanin cewa kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa na Ingila, Liverpool zasu gana da ‘yan wasan kwallon kafan Barcelona a Spain, ranar Laraba, 1 ga watan Mayu a fillin kwallon Barcelona ta Camp Nou don wasar su na Semi Final.

Gidan labaran nan tamu ta gane da cewa kungiyar wasan kwallon biyu na cikin manyan Kulob da ke cikin lokaci a halin yanzu. Ba mai iya bada tabbacin gwalagwalai ko yadda wasan zata kare a gobe sai har an kamala wasan.

Messi sananne ne kuma babban dan kwallon kafa ne kuwa a dukan duniya, amma bisa irin kokari da Virgil, dan kwallon Liverpool ke yi a wannan karon, ba mammaki ya iya dakatar da Messi daga motsi a wasan.

Ko da shike da manema labarai suka bukaci Virgil da bayani akan irin shiri da yake da shi na dakatar da Messi ga cin kwallo a wasa, sai ya ce “A gani na da sani na, Messi babban dan wasan kwallo ne a duniya gaba daya, dakatar da shi daga ci zai zama da wuyar gaske, amma idan har mun hada kai da juna a Kulob na mu, mun iya cin nasara ga wasar”

“Ba mu kare dan kwallo a dayantaka, mukan kare dan kwallo ne gaba daya dukan mu. Zamu shirya kwarai da gaske, wannan shafi ne na kusan karshen wasan Champions League.” inji Virgil.

Karanta wannan kuma: Muna da kudurin Fita takaran zabe nan gaba daga Kannywood – inji Ali Nuhu