Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 30 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 30 ga Watan Afrilu, 2019

1. Zaben 2019: PDP na zargin Hukumar INEC da musanya sakamakon zaben 2019 da ke a Kwanfutan su

Jam’iyyar PDP ta Tarayya na gabatar da sabon zargi ga Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben kasar Najeriya. PDP na fadin cewa INEC ta musanya sakamakon zaben da ke a kwanfutocin su a kowace jihar kasar.

PDP sun gabatar da zargin ne a wata gabatarwa da kakakin yada yawun Jam’iyyar, Mista Kola Ologbondiyan, yayi a ranar Litini da ta gabata.

2. Manyan Jam’iyyar APC sun dage da cewa Yahaya Bello bai dace da komawa shugabancin Jihar Kogi ba

Masu ruwa da tsaki ta Jihar Kogi daga Jam’iyyar shugabancin kasa (APC), sun dage da gayawa shugaba Muhammadu Buhari da cewa kada a bayar da dama ga Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, da komawa kujerar Gwamnan Jihar. ta karo biyu.

A bayanin ‘yan Jam’iyyar APC na Jihar, sun bayyana da cewa Gwamna Bello ya karbi kudi kimanin naira biliyan (N344billion) tsakanin watannai 38 da yayi jagoranci, amma ba wata abin nuni ga yadda Bello yayi amfani da kudaden ga ci gaban Jihar.

3. Hukumar NIS ta fara bayar da sabon Fasfot na Tafiye-Tafiyen kasa ga ‘yan Najeriya

Hukumar Sabis na Shiga da Fita na Najeriya, NIS sun fara bada sabon katin fasfot mai amfanin tsawon shekara goma da aka gabatar a baya ga ‘yan Najeriya.

Naija News Hausa ta gane da wannan ne a wata gabatarwa da  shugaban hukumar NIS, Mista Muhammad Babandede ya bayar a Hedikwatan Hukumar da ke a birnin Tarayya, Abuja.

4. Gwamnan Jihar Zamfara yayi gargadin kasa akan Sanin koma bayan tattalin arziki

Abdulaziz Yari, Gwamnan Jihar Zamfara ya gabatar da sabon hange da cewa ya gane da alamun cewa kasar Najeriya zata fuskanci koma bayan tattalin arziki a shekarar 2020.

Gwamna Yari ya bayyana hakan ne a wata gabatarwa da yayi a ranar Litini da ta gabata a wata taron tattaunawa da Gwamnonin Jihohin kasar Najeriya da aka yi a birnin Abuja.

5. A karshe, Akpabio da Amaechi sun amince da hada hannu don ci gaban APC

A karshe, Jigon Jam’iyyar APC biyu daga Kudu maso Kudu ta kasar Najeriya, Rotimi Amaechi da Godswill Akpabio sun zo ga arjejeniya don tabbatar da zumunci da cigaban Jam’iyyar APC a yankin su.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne bayan wata ganawa da Jigo biyun suka yi na amincewa da juna a birnin Abuja ranar Lahadin da ta gabata.

6. Yawar Al’ummar Najeriya ya karu da shiga kimanin mutane Miliyan 201m – inji UN

Hadaddiyar Kungiyar Tallafin Kasashe (UNFPA) sun bayyana da cewa kasar Najeriya na da kimanin yawar mutane Miliyan 201 a halin da ake ciki.

Naija News ta gane da wannan ne a wata Rahoto da ke a cikin takardan yawar Al’ummar kasa na hukumar UNFPA ta shekarar 2019.

7. Sabi da Tsohin Gwamnonin Jihohin kasar Najeriya sun gana a Abuja

Kungiyar Gwamnonin Jihohin kasar Najeriya (NGF) sun yi wata ganawa da kadamarwa a birnin Tarayya, Abuja.

Naija News Hausa ta samu sanin cewa zaman da Gwamnonin suka yi a fadar shugaban kasa ya samu halartan tsohi da sabbin Gwamnonin kasar.

8. APC da Shugabancin kasa na kokarin kauracewa dokar kasa ta  shekarar 1999 –  inji PDP

Jam’iyyar Dimokradiyya, PDP na zargin Jam’iyyar APC da Shugabancin kasar Najeriya da kokarin kaurace wa dokar kasar Najeriya da aka bayar a shekarar 1999 da ta gabata.

A wata bayani da kakakin yada yawun PDP, Kola Ologbondiyan, ya bayar ranar Litini da ta wuce, ya ce “Tafiyar shugaba Muhammadu Buhari na tsawon kwanaki goma a London ba tare da bayar da dama ga mataimakin shi da ci gaba da maye gurbin sa kamar yadda doka ta bayar ba, bai dace ba” Wannan karya dokar kasa ne, inji Mista Kola.

9. Dalilin da ya sa Buhari bai bayar da gurbin sa ga Osinbajo ba – Garba Shehu

Babban mataimaki ga shugaba Muhammadu Buhari ta hanyar sadarwa, Garba Shehu, ya gabatar da cewa shugaban na iya gudanar da kadamar da shugabancin sa a ko ina a duniya.

Naija News ta gane da cewa Garba ya fadi hakan ne don mayar da martani ga zargin da Jam’iyyar PDP ke yi na cewa shugaba Buhari ya karya dokar kasa akan rashin bada daman maye gurbi ga mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com