Connect with us

Labaran Najeriya

Sabuwa: An sace babban Malamin Makarantar Jami’a a Jalingo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Da safiyar yau Talata, 30 ga watan Afrilu, Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa wasu ‘yan hari da bindiga da ba a gane da su ba sun sace Mista Sanusi Sa’ad, mataimakin Rajistra na Makarantan Jami’a babba na Jihar Taraba da ke a Jalingo.

Bisa ga rahoton da aka bayar ga manema labarai, abin ya faru ne a missalin karfe daya (1am) na safiyar ranar yau, Talata, 30 ga watan Afrilu 2019, anan gidan shi da ke a mazaunin Malaman makarantar Jami’ar.

Naija News Hausa ta samun tabbacin hakan ne bisa bayanin da Ciyaman na Kungiyar Malaman Makarantar Jami’a babba na Jihar Taraba, Dakta Samuel Shikaa, ya bayar ga manema labaran Punch da ke a Jalingo akan wayar Salula.

A fadin Dakta Shikaa, ya bayyana da cewa ‘yan harin sun fada cikin gidan Mista Sanusi ne ta kofar bayar gidan, suka kuma sace shi ba da sanin kowa ba ko ta ina suka tafi da shi.

A halin yanzu Babban Makarantar Jami’ar Taraba a karkashin kungiyar ASUU na cikin yajin aiki akan matsalar rashin tsaro ta musanman da babu shi a Jihar.

Amma dai, Kwamishanan Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Taraba, Mista Alkasim Sanusi, a yayin da yake kafa rukunin tsaron ‘Operation Puff Adder’, ya gargadi ‘yan hari da makami da ‘yan ta’addan Jihar Taraba da janyewa daga hare-haren da suke yi a Jihar, ya kuma yi barazanar cewa idan har suka dage basu bar hakan ba, zai tabbatar da cewa ya tsananta masu da ganin cewa ya magance su.

Karanta wannan kuma: Sheikh El-Zakzaky da Matarsa na bukatan mu tafi dasu kasar Turai don karin kulawa – Dakta Kazim Dhalla