Connect with us

Labaran Najeriya

Sheikh El-Zakzaky da Matarsa na bukatan mu tafi dasu kasar mu don karin kulawa – Dakta Kazim Dhalla

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa wasu Daktoci daga kasar Turai sun shigo Najeriya don binciken lafiyar jikin Sheikh El-Zakzaky da Matarsa da ke a kulle.

A yau mun samu rahoto kamar yadda aka bayar ga manema labarai da cewa Daktocin sun gabatar da cewa ya zama dole su tafi da shugaba Kungiyar ‘Yan Shi’a (IMN), Ibraheem El-Zakzaky da Uwar gidan sa don bashi kulawa ta gaske.

Daktocin sun bayyana hakan ne bayan binciken ‘yan kwanaki da suka yi wa Sheikh Ibrahim da da Matarsa Zinat.

“Sheikh El-Zakzaky da Matarsa na bukatan mu tafi da su kasar Turai, su biyun na da cututtukar da dama da ya bukaci hakan” inji bayanin Daktocin ga manema labarai.

Daya daga cikin Daktocin, Kazim Akber Dhalla, Dakta mai kula da Ilar Ido, ya ce “Bisa bincike da kulawa da muka yi wa Sheikh da Matarsa, mun gane da cewa su biyun na da Illar jiki da yawa da ke bukatar kulawa ta musanman a kasar Turai.” inji Shi.

“Mun rigaya mun basu kulawa akan wasu daga cikin cutukan, amma a ganewar mu bisa bincike, suna bukatar mu tafi da su kasar Turai don karin kulawa musanman da Manyan Na’urai da zamu yi amfani da su da babu shi anan kasar, sai dai can.”

Naija News Hausa ta gane da cewa wannan shiri da matakin ya biyo baya ne bayan da Seyed Mousavi, kakakin yada yawun kasar Iran ya rattaba da Jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari, bisa kokarin da yayi na bada dama ga Daktoci daga kasar Turai don binciken lafiyar jikin Sheikh Ibrahim da Matarsa Zinat.

Ka karanta wannan kuma; Shugaban Miyyeti Allah na Jihar Bauchi yayi bayanin game da kashe kashen da ake yi a Jihar