Connect with us

Labaran Najeriya

Tafiyar Buhari zuwa Turai ba tare da barin Osinbajo ya maye gurbin sa, ba daidai bane – PDP

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Naija News Hausa, Labaran Shugaba Muhammadu Buhari, Labaran Najeriya a Yau, Labaran Hausa, Shugabancin Kasar Najeriya

Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) na kalubalantar shugaba Muhammadu Buhari da yin tafiya zuwa kasar Turai ba tare da bada daman ci gaba da shugabanci ga mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo ba.

Naija News Hausa ta ruwaito a wata labarai a baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyarar kai tsaye a kasar Turai, inda aka bayyana da cewa shugaban ba zai dawo kasar Najeriya ba sai har zuwa ranar 5 ga watan Mayu ta 2019.

Ko da shike ba a bayyana dalilin tafiyar shugaban ba, amma an gabatar da cewa ziyarar na kai tsaye ne kuma zai dauki tsawon kwanaki goma kamin ya dawo.

Ko da shike dai bisa jita-jitan mutane, Naija News Hausa na tsanmanin cewa wata kila shugaban ya ziyarci kasar Turai ne don binciken lafiyar jikin sa.

Amma abin kula shine da cewa shugaba Muhammadu Buhari bai bada dama ga mataimakin sa Farfesa Osinbajo ba, kamar yadda ya saba, kuma kamar yadda doka ta bayar.

“Matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na rashin bada gurbin sa ga mataimakin sa a yayin da baya a kasar Najeriya, ba daidai bane. Dokar kasa ta bukaci shugaba ya bada dama ga mataimakin sa da daukan matakai a yayin da shugaba zai fita kasar, amma rashin yin hakan ga shugaba Buhari ya nuna da cewa da shi da Jam’iyyar APC basu damu da bin dokar kasa ba, kuma basu da ra’ayin al’ummar kasar a zuciyar su” inji bayanin Mista Kola Ologbondiyan, kakakin yada yawun Jam’iyyar PDP na Tarayya.

KARANTA WANNAN KUMA: Ba da gangan na ki bayyana ga Ziyarar Buhari ba a Legas – inji Tinubu

Jam’iyyar Adawa, PDP sun bayyana da cewa irin wannan tafiya na shugaba Muhammadu Buhari da bai da wata kwakwarar dalili ko manufa ba daidai bane, musanman irin hali da yanayin da ake ciki a kasar a wannan lokacin.

“Bai dace ba ga shugaba Buhari da yin watsi da lamarin kasar Najeriya ba da shiga tafiya mara dalili, musanman a halin matsalar tsaro da mawuyacin yanayi da ake a ciki a kasar. Wannan ya bayyana irin yanayin da kasar Najeriya zata kasance nan gaba idan har aka bada dama ga Buhari da Gwamnatin sa da ci gaba da mulkin kasar.” inji PDP.

Ko da shike a yayin da Jam’iyyar PDP ke gabatar da zargin ziyarar Buhari a UK ba tare da mayar da gurbin sa ga mataimakin sa ba, an rufe bakin su da fadin cewa ai ba Buhari kawai ba, har ma tsohin shugabannan kasar da suka yi mulki a baya sun yi hakan, musanman daga jam’iyyar PDP.

An gabatar da cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo da Marigayi Umar Yar’Adua da suka yi shugabancin kasar Najeriya a karkashin Jam’iyyar PDP a baya sun yi hakan. Sun fita daga kasar Najeriya zuwa wata kasa ba tare da bada dama ga mataimakan su da ci gaba da mulki ba kamin su dawo.