Connect with us

Uncategorized

Wasu ‘Yan Hari da Makami sun sace Dakta Muhammad Abubakar Ciyaman na UBEC

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jami”an tsaron ”Yan Sandan Jihar Kaduna sun bada tabbacin sace Ciyaman na Kungiyar UBEC da wasu Mahara da makamai suka sace a hanyar da ta bi daga Abuja zuwa Kaduna.

Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa wasu ‘yan hari da bindiga da ke sanye da kakin sojojin Najeriya sun hari motar Dakta Muhammad Abubakar da diyar sa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, ranar Litini da ta gabata.

Kakakin yada yawun Jami’an tsaro, DSP Yakubu Sabo, a wata sanarwa da ya bayar ranar Litini da ta gabata, ya ce “Hukumar ‘yan sanda da ke a rukunin Katari sun karbi wata kirar gaugawa da cewa wasu ‘yan hari da bindiga da ke sanye da Kakin sojoji sun tare wata motar Land Cruiser da Toyota Sienna a hanyar da ta bi daga Abuja zuwa Kaduna.”

Ya bayyana da cewa DPO da ke a rukunin tsaro ta Katari ya kira su ne a ranar 29 da watan Afrilu, 2019 a missalin karfe Ukku da rabi (3:30pm) na tsakar ranar Litini da ta gabata, da cewa wasu mahara sanye da kakin rundunar sojojin Najeriya sun tari motoci biyu a nan kauyan Kurmin Kare da ke a kan babban hanyar da ta bi Abuja zuwa Kaduna.

“Sun hari motar da ke gaba da harbin bindiga har sai da suka kashe direban motar, suka kuma sace mai motar, watau Dakta Muhammad Abubakar, Ciyaman na Kungiyar UBEC da diyar shi.

A halin yanzu anan kan bincike game da harin, idan akwai wata karin bayani da ya biyo baya, zamu sanar da shi a shafin mu na Hausa.NaijaNews.Com