Connect with us

Uncategorized

Abin Takaici: An iske Gawar Yara Ukku cikin wata Mota bayan ‘yan kwanaki da bacewar su

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu Iyalai na cikin bakin ciki da hawaye a yayin da aka gano diyan su macce a cikin mota, bayan shigewar awowi ta rana daya da aka gabatar da bacewar su.

Bisa bincike da ganewar manema labarai, an bayyana da cewa yaran na wani mutumi ne mai suna Jackson Bobo, tsohon ciyaman na ‘yan Kabu-kabun shiyar.

An gano da gawar yaran ne cikin motar Mista Bobo da ya faka a gaban gidan sa, bayan tsawon awowi da dama da aka gabatar da bacewar su.

“A shiga binciken yaran tun jiya da aka gabatar da bacewar su, kwaram sai aka iske su cikin motar Mista Bobo da ya faka a gaban gidan sa a ranar ta biyu.” inji mai bada bayani ga manema labarai.

An bayyana da cewa biyu daga cikin yaran haifuwar Mista Bobo ne, amma na ukkun an baiwa daya daga cikin matan shi ne don reno.

A halin yanzu Jami’an tsaro na kan bincike akan al’amarin don gane mafari, yadda aka sace yaran da kuma wanda yayi kisan su.

Kalli hotuna a kasa;

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Jami’an ‘Yan sandan Najeriya ta rukunin Birnin Tarayya, Abuja, sun kame wani mutumi mai suna Yakubu Mohammed a shiyar Nyanya a yayin da yake kokarin sace wata Mota.