Connect with us

Uncategorized

Farmaki ya tashi a Jihar Filatu, An kashe Mutane Ukku, An kuma kashe Shanaye fiye da 300

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi sabuwar labari da cewa farmaki ya tashi a Jihar Filatu a ranar Talata da ta wuce, inda aka bayar da cewa kimanin mutane Ukku aka kashe a farmakin, sa’anan kuma aka dauke rayukan shanaye fiye da 300 a yankuna  ukku a Jihar.

Abin ya faru ne a yankuna ukku a Jihar, na daya itace a kauyan Kuru, ta biyu kuma Maiyangan da ta ukkun Rekwechungu a shiyar karamar Hukumar Bassa.

Bisa zargin Kungiyar Fulanin Jihar Jos da aka fi sani da Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), da kuma Kungiyar Fulani da ake kira Jonde Jam Fulani Youth Association sun gabatar da zargin cewa wata rukunin ta’addanci ne da ake kira Irigwe daga shiyar Miyango suka aiwatar da harin.

Ciyaman na kungiyar MACBAN, Muhammad Nuru Abdullahi ya bayyana ga manema labarai da cewa sun gano Matattatun Shanaye 29 a shiyar Kuru da safiyar ranar Talata sa’anan kuma sun gano da wasu matattun shanaye 314 kuma a yankin Maiyanga, kusa da makarantar Jami’ar ‘School of Accountancy’ da ke a karkaran Kwal ta karamar hukumar Bassa.

Mista Abdullahi ya bayar da cewa an kashe Shehu Saedu, sa’anan kuma wani mai suna Mubarak Adamu ya bata a harin.

Ya bayyana da cewa shanayen da aka kashe ba na mutum daya bane, sun hade ne da na Mista Dauda Jalo, Malam Inusa Jalo, Malam Mohammed Adam, Malama Sani Alhassan, Malam Abdulkadir Saeed, Malam Kabiru Mohammed, Malam Yakubu Mahmud da kuma Malam Auwal Abubakar.

Da aka bukaci bayani daga Kwamandan Jami’an tsaron rukunin ‘yan sandan Jihar ta ‘Operation Safe Haven’ Major General Augustin Agundu, ya ce “Wannan harin abin takaici ne kwarai da gaske”, ya kuma nuna bakin cikin shi da hakan.

Ko da shike bai bayyana ko mutane da shanaye nawa ne suka mutu ba.

Karanta wannan kuma; Bayanin Shugaban Miyyeti Allah game da kashe kashen rayuka a Jihar Bauchi