Connect with us

Uncategorized

Ga wata: Boko Haram sun kashe Kimanin mutane 14 a Borno

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan Ta’addan Boko Haram sun kai sabuwar hari da kashe mutane 14 a yankin Monguno ta Jihar Borno

Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun hari shiyar Monguno a Jihar Borno inda suka kashe kimanin mutani 14 a yayin da suke yanka da tara itace cikin gonaki a Arewa masu gabashin kasar.

An gano gangar jikin mutanen ne a shiyar kauyan Duwabayi da ke kusa da Monguno, ranar Talata da ta wuce.

A halin yanzu an riga an kai gawakin mutane 14 a Ofishin Jami’an tsaron yankin Monguno.

“An kawo gangar jikin mutane goma shahudu ne da maraice a garin Monguno, tun daga lokacin kuma mutane na zagayar Ofishin ‘yan Sandan don wata kila a gane su,” inji bayanin wani mazaunin Monguno, Kulo Gana.

Bisa bayanin wani mazaunin shiyar mai suna Bunami Mukhtar, ya bayyana da cewa ya gane gawakin da raunukan harsashen bindiga.

Naija News Hausa ta sanar a baya da cewa wasu ‘yan hari da makamai sun hari kauyan Guzurawa da ke a karamar hukumar Safana a Jihar Katsina, a ranar Lahadi da ta gabata, inda suka kashe wani tsoho mai tsawon shekaru 80 da haifuwa da ke a Unguwar Duwa, ta kauyan Guzurawa.