Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 1 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 1 ga Watan Mayu, 2019

1. Gidan Majalisar Dattijai sun gabatar da kasafin kudin kasa ta shekarar 2019

A ranar Talata da ta gabata, Gidan Majalisar Dattijai sun gabatar da kasafin kudin Najeriya ta naira Tiriliyan N8.916 na shekarar 2019.

Naija News ta gane da cewa wannan kasafin kudin kasar ya fiye da kasafin kudi da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a baya na naira Tiriliyan N8.83.

2. Kungiyar Gwamnonin Najeriya sun hana Manema labarai da shiga taron su

An hana Manema labarai daman shiga dakin taron Gwamnonin Jihar Kasar Najeriya a wata hidimar ganawa da tsohi da sabbin Gwamnonin ke yi a birnin Abuja.

Naija News Hausa ta sanar a Manyan Labaran Jaridun Najeriya a baya da cewa Gwamnonin Jihohin kasar Najeriya na wata ganawa.

3. Ciyaman na Kungiyar UBEC da diyar shi sun samu kubuta daga hannun Mahara da Bindiga

Naija News Hausa ta karbi rahoto da tabbacin cewa Ciyaman na Kungiyar (UBEC) da aka sace a baya, Dr. Muhammad Abubakar ya samu kubuta daga hannun ‘yan harin.

Mun samu tabbacin hakan ne a wata sanarwa da Sanata Shehu Sani, da ke wakilcin Jihar Kaduna ya bayar a ranar Talata da ta gabata na cewar Dakta Abubakar da diyar sa sun kubuta daga hannun maharan.

4. Yanzun aka fara, Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya kalubalanci Sanata Dino Melaye

Gwaman Jihar Kogi, Gwamna Yahaya Bello ya kalubalanci Sanata Dino Melaye, dake wakilcin Yammacin Jihar Kogi a gidan Majalisar Dattijai.

Naija News Hausa ta gane da cewa wannan ya biyo ne bayan da Dino ya zargi Gwamna Bello da kin biyar kudin ma’aikata da kuma shirin cin bashin Miliyoyi kan asusun Jihar.

5. Bayanin Atiku game da Ranar Hutun Ma’aikatan Kasar Najeriya

Dan takaran kujerar Shugaban kasar Najeriya a zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya gabatar da gaisuwar musanman ga Ma’aikatan kasar Najeriya akan bikin Ranar Ma’aikata ta ranar yau, Laraba, 1 ga watan Mayu.

Atiku ya gabatar da gaisuwar ne a wata sako da ya wallafa da kuma rattaba hannu, wanda ya aika a gidan labaran mu ta Naija News. Dan takaran ya jinjina wa Ma’aikatan Najeriya da kokari da yaki da karfafa Tattalin Arzikin kasar Najeriya.

6. Saudi Arabia sun saki ‘yar Najeriya, Zainab Aliyu da suka kame a baya

An sanar a ranar Talata da cewa kasar Saudi Arabia sun saki Zainab Habib Aliyu da suka kame a baya akan wata laifi da ake zargin ta da shi.

Naija News Hausa na da sanin cewa an zargi Zainab ne da kadamar da ayukan ajiyar da sayar da mugayan kwayuka a kasar Saudi.

7. Gidan Majalisar Dattijai sun kara Naira Biliyan N100b ga kasafin kudin Najeriya ta shekarar 2019

Naija News na da sanin cewa Shugaba  Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2019 ta naira Tiriliyan N8.83tr a baya.

Majalisar Dattijai a ranar Talata da ta gabata sun gabatar da sabon kasafin kudin kasar ta naira Tiriliyan N8.916tr wanda ya bayyana da cewa sun kara bisa ga wanda shugaba Buhari ya gabatar a baya.

8. ‘Yan Ta’addan Boko Haram na karban kudin dala $3,000 a kowace rana – inji Mohammed

Sidi Ali Mohammed, Mamba daga Kwamitin Shugaban kasa a Arewacin kasar Najeriya, ya gabatar da cewa ‘yan ta’addan Boko Haram na karban kudi dala dubu ukku $3,000 a kullum, fiye da naira dubu daya N1,000 da ake baiwa Rundunar Sojojin Najeriya da ke yaki da ta’addancin kasar.

Mista Ali ya bayyana hakan ne a wata gabatarwa da ya bayar a ranar Litini da ta gabata a birnin Abuja.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com