Connect with us

Uncategorized

An Sace Mutane shidda a yayin da ake Kallon wasan Barcelona da Liverpool

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mahara sun kai Sabuwar Hari a Jihar Zamfara

Naija News Hausa ta karbi sabon rahoto da safen nan da cewa wasu ‘yan hari da bindiga sun sace kimanin mutane shidda a wata makarantan mata a Jihar Katsina.

Wannan abin ya faru ne a daren ranar Labara, 1 ga watan Mayu 2019 da ta wuce a yayin da ‘yan makaranta da ‘yan unguwa ke kallon wasan kwallon kafa da aka buga a daren jiya tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ta Liverpool.

An bayyana da cewa ‘yan harin sun sace Malaman makarantar guda biyu da kuma sace Mata hudu da ke kula da ‘yan makarantar.

Ko da shike maharan basu samu isa gidan kwanan ‘yan makarantar ba a yayin da ake cikin kallon wasan kwallon kafar UEFA Champions League. Amma bai an kara da cewa sun samu kashe mutum daya a lokacin da suka bude wutar bindiga a shiyar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘yan fashi sun fada gidan tsohon dan wasan kwallon kafa ta Najeriya, Kanu Nwankwo, sun kuma kwashe kayakin adon da ke cikin gidan, harma da kyautannai masu tsadar gaske da ya samu a lokacin da ya saura da wasan kwallon kafa.

Wannan ya faru ne a gidan Kanu da ke a hanyar Waziri, a Victoria Island ta birnin Legas, inda ya ajiye wadannan kayakin, da kyautuna da ya karba, sakamakon kwarewansa a fagen wasan kwallon kafa, shekaran baya da suka shige.