Connect with us

Labaran Najeriya

Ana wata ga Wata: ‘Yan Hari sun sace Surukin Shugaba Muhammadu Buhari

Published

on

at

Wasu Mahara da bindiga da ba a gane da su ba sun sace Alhaji Musa Umar, Sarkin Daura, a maraicen ranar Labara da ta gabata.

Naija News ta samu ganewa da cewa ‘yan hari da makamin sun hari gidan Sarkin Daura ne a missalin karfe Bakwai na maraicen ranar Laraba, suka yi ta harbe-harbe a iska don bada tsoro ga mutane kamin suka sace Alhaji Musa.

Bisa ganewa, ‘Yan harin sun fada gidan Alhaji Umar ne bayan dawowar sa da ibada daga Masallaci.

Wani mazaunin Shiyar da ya samu ganawa da ala’amarin ya bayyana ga manema labarai da cewa Alhaji Umar na zaune ne da wasu mutane a kofar fadar sa kamin ‘yan hari da makamin suka fado masu da hari.

“Maharan sun haro gaban gidan Alhaji Umar ne da wata Motar Peugeot mai lamba 406 da harbe-harben bindiga”

“Bayan wucewar ‘Yan Harin, Ciyaman na Kwamitin Daura, Malam Abba Mato da tulin mutanen unguwar sun haro gidan Alhaji Umar da gane da cewa an riga an tafi da shi.”

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Hukumar tsaro sun ci nasara da kame ‘yan hari da makami da suka sace Sheikh Ahmad Sulaiman kwanakin baya.

An gabatar da kame Lawal Ibrahim ne da mambobin kungiyar ta’addancin a yayin da suke kokarin shiga yankin Jihar Kogi.