Connect with us

Uncategorized

Kalli Kyakyawan Amfanin Tafarnuwa da baka sani ba

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Amfanin Man Tafarnuwa

Jerin Amfanin Man Tafarnuwa ga Al’umma

1-  Yaki da Ciwon Mara:

Duk Macce da ke Al’ada da kuma jin maran ta da ciwo lokacin al’ada, ko kuma tana jinin yarika yi mata wasa,

Abin yi shine;

  • Ta nemi zuma ludayi biyu, ta hada da man tafarnuwa ludayi daya, idan ta yi hakan sai ta rika sha cokali biyu da safe, biyu kuma da yamma har sai ciwon ya wuce da yardan Allah.

2. Zubar Jini ga Macce

Macce da Jini ya ki dauke mata ta rika daukan wannan mataki;

  • Ta rika shan man tafarnuwa babban cokali sau hudu [4] a rana. Da izinin Allah zubar jinin zai dauke

3. Riga kafin Ciwon Nono Ga Wadda Tahaihu

Matakin dauka ga macce da ke ciwon nono bayan ta haifu:

  • Ta dinga cin dabino guda bakwai [7]
  • Ta sha man tafarnuwa, babban cokali uku [3] a rana zuwa tsawon kwana uku [3]. Idan an yi hakan da izinin Allah za a dace.

4. Daurewar Ciki Ko Mara Bayan Haihuwa

  • Ta samu ruwan zafi kofi daya, ta zuba man tafarnuwa babban cokali daya, ta dinga sha sau uku a rana har tsawon kwanaki uku, da yaddan Allah zai barta.

5. Yawan Lalacewar Ciki Ko Yawan Bari

A nemi kwan agwagwa, a hada da man tafarnuwa, sai a soya. A gwada baiwa matar ta ci sau biyu a rana har tsawon kwanaki bakwai.

6. Tsawon Gashi Da Hana Shi Karyewa

Idan ka ko kin damu da sumar ki, kana ko kina iya samun man kwakwa, sai a hada da man zaitun da kuma man tafarnuwa, a tabbatar da cewa man tafarnuwa yafi yafa cikin hadin. Idan an yi hakan sai a dinga shafawa a kai.

Cikin ‘yan kwanaki kadan da ikon Allah za a ga sake wa.

7. Tari Ko Wanne Iri

Amfani da man tafarnuwa da man zaitun, hade da Zuma mai kyau na magance Tari. A tabbatar da cewa zuma yafi yawa bisa sauram, sai a hada su waje guda, a jijjiga sa’anan asha cokali biyu da safe, biyu da rana sannan kuma da yamma.

Da yardan Allah, za a samu sauki daga ciwon Tari.

8. Hawan jini Ko Rashin Yin Barci Mai Kyau

Hawan Jini mumunar abu ne kwarai da gaske, amma duk da hakan Allah kan bada nasara da shi musanman idan anyi amfani da hikimar da Allah ya bayar.

Yadda zaka yi amfani da Tafarnuwa don magance hawar jini shi ne kamar haka;

Ka samu garin Tafarnuwa rabin ludayi da zuma mai kyau, sai ka hada su waje daya kana gaurayawa. Ka sha cokali babba daya sau uku (3) a rana. Bayan hakan kuma ka yi ta shafa man tafarnuwa a jikinka ko jikin ki.

Idan an gwada hakan cikin ‘yan kwanaki kadan, Allah zai nuna ikon sa, zai kuma bada lafiyar jiki.

Ka bi layin Hausa.NaijaNews.Com don samun kyakyawan labaran Hausa da labaran Najeriya a koyaushe.