Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 3 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 3 ga Watan Mayu, 2019

1. PDP/APC: Dalilin da zai sa Atiku ya nemi karban yancin sa – SAN

Babban Magatakarda na Najeriya (SAN), Chris Uche, da ke jagorancin karar Dan takaran shugaban kasa na shekarar 2019 daga Jam’iyyar Dimokradiyya PDP, Alh. Atiku Abubakar, ya bayyana dalilin da zai sa ya zama dole ga Atiku da neman karban yancin sa.

Naija News Hausa na da ganewar cewa Atiku da ‘yan Jam’iyyar PDP na gwagwarmaya da kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar 2019.

2. Kungiyar FAAN sun dakile Gidan Sauka da Tashin Jirgin Sama a Jihar Gombe da Kebbi

Hukumar Filin Jirgin Sama ta Tarayyar Kasar Najeriya (FAAN) sun dakile Filin Jirgin Sama ta Jihar Gombe da Jihar Kebbi akan wata bashi na naira Miliyan N800.

Wannan ya faru ne a yau bayan da Hukumar ta bada umarni ga Kamfanonin Filayan Jirgin Saman da cewa su tabbatar da biyar basussukar su kamin ranar 24 ga watan Afrilu da ta gabata.

3. Jami’an Tsaro sun kame wadanda suka sace ADC na shugaba Buhari

Hukumar Jami’an tsaron Jihar Katsina sun gabatar da cewa sun kame ‘yan hari da makami da ake zargi da sace babban Ma’aikacni Tsaro ga shugaba Muhammadu Buhari.

Naija News ta ruwaito a baya bisa wata sanarwa da kakakin jami’an tsaron Jihar Katsina, Gambo Isah ya bayar da cewa ‘yan hari da makami sun sace Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Uba, a ranar Talata da ta wuce a gidansa.

4. Kungiyar IPOB sun gabatar da dokar Kuntatawa ga ranar  30 ga watan Mayu

Kungiyar ‘Yan Iyamirai da ke yaki da neman yancin Biafra (IPOB), sun gabatar da ranar 30 ga watan Mayu ta shekarar 2019 a matsayin ranar ranar zama daki kulle ga ‘yan Biafra don tunawa da Manyan su da suka mutu a baya.

Kungiyar kuma sun bukaci dukan Addinai don taimaka da addu’a gabadin ranar, don tunawa da manyan ‘yan Biafra da aka kashe a baya wajen yaki.

5. ‘Yan Hari da Makami sun hari Makarantar ‘yan Mata a Zamfara, sun kashe mutum daya, da sace wasu

Wasu ‘yan Hari da Makami sun hari Makarantar Sakandari na Government Girls Secondary School da ke shiyar Moriki, ta karamar hukumar Zulu a Jihar Zamfara.

Bisa ganewa da yadda aka bayar ga manema labarai, An bayyana da cewa ‘yan harin sun sace Malaman makarantar guda biyu da kuma sace Mata hudu da ke kula da ‘yan makarantar.

6. Bayanin shugaba Muhammadu Buhari ga Manema Labaran Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi Manema Labaran Najeriya da ci gaba da samar da ayukan su a kasar akan dokar da hukumar kungiyar ta bayar.

Shugaba Buhari ya gabatar da hakan ne a wata gabatarwa da ya bayar a ranar Alhamis da ta gabata daga bakin Mista Femi Adesina, babban mataimakin shugaban wajen lamarin sadarwa.

7. PDP/APC: Atiku ya gargadi Buhari akan yadda zai samu takardan WAEC din sa

Dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gargadi shugaba Muhammadu Buhari game da takardun WAEC na sa.

“Ka bada umarni ga Rundunar Sojoji don su nemo maka takardan WAEC naka idan ma akwai shi” inji Atiku.

8. Ka dawo gida don Dakatar da Kashe-Kashen rayuka, PDP sun gayawa Buhari

Jam’iyyar Dimokradiyya, PDP sun kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari da cewa ya komo Najeriya don magance matsalar da kasar ke a ciki.

Wannan itace bayanin PDP a ranar Alhamis da ta gabata da Kakakin yada yawun Jam’iyyar PDP, Mista Kola Ologbondiyan ya bayar, da cewa “Bai dace ba yadda shugaba Muhammadu Buhari ya fita kasar Najeriya zuwa ziyarar wata kasa a yayin da kasar Najeriya ke cikin mawuyacin hali.”

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com