Connect with us

Uncategorized

Ire Iren ‘Ya’yan itãcen marmari da ya dace a ci lokacin Bude Baki

Published

on

‘YA’YAN ITACEN MARMARI DA KE DA KYAU GA CI LOKACIN AZUMI

Allah ya baiwa kasar Najeriya ‘ya’yan itace da dama da ke da kyan gaske da kuma gina lafiyar jikin mu.

A yayin da aka soma Azumin  bana, ya dace ka ko ki san irin ‘ya’yan itace da ke da kyau da kuma iya gina jiki, musanman lokacin shanruwa.

Mun sanar a shafin labaran mu da safen nan da cewa Mai Martaba, Sultan na Sokoto ya sanar da cewa za a fara Azumi a yau Litini, 6 ga watan Mayu ta shekarar 2019, bayan da aka gane da fitar watan Ramadan a Jihar Sokoto.

Mun gane a Naija News Hausa da cewa ya dace mu gabatar da ‘ya ‘yan itace masu gina jiki, da kuma ya dace a ci idan lokacin Shanruwa ya kawo.

Ga su nan kamar haka;

 • DABINO

Dabino sanannen ‘Ya’yan itace ne da ‘yan Najeriya gaba daya suka fi ci lokacin Azumi.

Dabino dan itaciya ne mai albarka da gaske, musanman ma Allah Madaukakin Sarki ya ambace shi a gurare da yawa cikin Alqur’ani mai girma.

AMBATON DABINO A SUNNAR MANZON ALLAH (SAW)
Wannan ya bayyana ne inda Manzon Allah – (SAW) yake cewa, “Idan kun kai azumi, to ku yi buda baki da dabino, amma idan bai samu ba to ya yi amfani da ruwa, domin ruwa na tsarkakewa.”

 • KANKANA

Kankana uwar ruwa, Kankana tafi amfani ne a lokacin da ta nuna sosai don masana sun ce sinadaran nunannar ya fi taruwa sosai musamman beta-carotene dake cunkushe a cikin jan tozon nan wanda ke matukar taimaka ma idanu. Zakin cikinta kuma na ba mutum karfi, tana kuma kara ma jiki ruwa.

Ga wasu Taimakon da Kankana ke yi a jikin mu kamar haka;

 1. – Nunannar kankana na taimaka ma fata saboda sinadarin lycopene dinta.
 2. – Sinadarin arginine dake cikinta na kara yawan nitric oxide dake kara ma namiji karfin gaba.
 3. – Sinadarin vitamin C dinta na taimako wajen maganin cututtuka da dama.
 4. – Tana maganin ciwon daji kala-kala, da kuma ciwon koda.
 5. – Nitric oxide da wasu sinadaren kankana na taimakon masu ciwon zuciya da hawan jini.
 6. – Tana haifar da samuwar wadataccen barci.
 7. – Tana da sinadarai masu kara karfin kashi (bone) da kuma maganin kumburin jiki musamman gabban jiki (joints).
 • LEMU

Lemu ya kunshi abubuwa da yawa a Cikinsa kamarsu; Citric acid, calcium,magnesium, Vitamin C, bioflavonoids, pectin da limonene. dukan wadannan na kawo kariya ga jiki da kuma yaki da cututtuka.

A lokacin da mutum ke Azumi jikin sa kan rasa ruwa sosai, Shi yasa Idan an sha Ruwa zakaji abubuwa da yawa na damun ka kamarsu: gajiya, rashin karfi, rashin karfin kayan yakin jiki, rashin kuzari, rashin barci, rashin tunani mai kyau da sauransu.

Idan ka sha Lemu kawai ko ka hada shi da ruwan dimi, ya kan mayar da wayannan ruwan da mutum ke rasawa a tsawon lokacin da ya dauka yana Azumi.

Bincike ya nuna Vitamin C dake cikin lemu, yana inganta warkewar ciwuka, kuma yana inganta lafiyar kasusuwa da sauransu. Yana taimako kwarai wajen inganta lafiya mai kyau.

 • KARAS

Karas yana daya daga ciki ‘yan itace da ake ci kwarai da gaske a Najeriya. Karas na da matuqar amfani ga jikin dan adam, musamman ga karfafa ganin idanu, don yana da Vitamin A, ko na ce Beta Carotene, wanda yake da matuqar mahimmanci wajen gyara ganin ido.

Karas na da amfani da gaske wajen taimaka da yaki da kumburin leben idanun, koda yake mu ‘yan Afurka ba mu san wannan matsalar ba, galibi mun fi gani a wajen Turawa in sun tsufa, ko Hindiyawa, to Karas kam yakan ba da gudummuwa hatta ga qwayan idanun shi kansa, akwai mutane da dama, ko na ce marubuta da masu bincike da suka tabbatar da cewa ba qaramin amfani Karas yake da shi ga ido ba, sai dai wannan maganar za ka yi mamaki in ka ji yadda wasu suke mu’amalla da ita, wasu ma cewa suka yi amfanin da ake samu ta hanyar gamsasshen barci ya fi wanda ake amfanuwa da shi ta hanyar Karas.

 • AYABA

Ayaba na da matukan amfani da yawa wajen gina jikin dan Adam

Maganin Hawan jini

Sanadiyar sunadarin potassium a da ke cikin ayaba, ya sanya ta na matukar tallafawa wajen rage hawan jini ga wadanda su ka manyanta.

Yaki Ciwon Zuciya da koda

Ayaba tana kunshe da sunadaran fiber, potassium, vitamin C da B6. Wadannan na bayar da kariya ga lafiyar zuciyar dan Adam. Binciken asibitin St Thomas dake garin Tennessee a kasar Amurka, ya bayyana cewa, wadannan sundaran su na taimakawa wajen yakar cututtukan zuciya da na koda a jikin a dan Adam.

Yaki da Asma

A wani bincike da aka gudanar a kwalejin ilimi ta kasar Landan, ya nuna cewa yara da suke cin ayaba kwara guda a rana, tana hana su kamuwa da cutar asma.

Yaki Cutar Kansa

Ci da Amfani da ayaba a shekaru biyun farko na rayuwar mutum yana hana kamuwa da cutar daji ta cikin jini. Akwai sunadarin vitamin C da yake yakar duk wasu kwayoyin cutar daji a jikin mutum.

_______________________________________________________________________________________________________________________

Ba wadannan kawai ba, akwai su da dama. Gargadi daga Naija News Hausa, ka tabbatar da cewa kowace ‘ya’yan itace zaka ci a wannan lokaci, ya zama mai kyau, ba wanda ya lallace ba, don lafiyar jikin ka ko jikin ki.

Allah ya sa a Gama Azumi Lafiya, ya kuma amsa Du’a’in mu duka. Amin.