Connect with us

Uncategorized

‘Yan Sandan Jihar Neja sun kame Mutum Ukku daga gida guda da zargin Kisa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi wata rahoto bisa gabatarwan manema labaran Punch da cewa Hukumar ‘yan Sandan Jihar Neja sun kame wasu ‘yan uwa ukku da laifin Kisan kai a karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.

An bayyana da cewa su ukkun sun sace wani ne mai suna Shehu Garba daga karamar hukumar zuwa wata wurin da ba wanda ya san da su, don amfani da shi wajen Maganin Kudi.

Ga sunayan ‘yan mutane Ukkun, ‘yan haifuwan gida daya;

  • Saminu Usman – Da shekarun haifuwa 25
  • Yusuf Usman    – Da shekarun haifuwa 22
  • Muhammadu Usman – babba daga cikin su, mai shekarun haifuwa 35

Dukan ‘yan gida guda ne daga kauyan Janruwa, a karamar Hukumar Borgu.

Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Jihar daga rukunin tsaron New Bussa ne suka sami kame ‘yan kisan kan, bisa sanarwa da kiran gaugawa da Malam Yakubu Garba, tsohon mutumin da aka kashe yayi ga Jami’an tsaron shiyar da cewa an sace yaron shi.

Manema labarai sun bayar da cewa bayan da su ukkun suka sace Shehu, sai suka tafi dashi cikin wani daji, inda suka kashe shi, suka kuma gunce masa hannu don amfani da shi wajen Maganin kudi da suke shiri da bukatar yi.

“Ba bukatar muke da mu kashe shi ba a da. Amma mun kashe shi, mun kuma gunce masa hannu don shirin amfani da shi ga Maganin Kudi kamin dada muka fada hannun Jami’an tsaro” inji daya daga cikin ‘yan kisan kan.

“Ban san abinda zan fada ba; mun bada Iyayen mu da dukan Iyalan mu duka da abokan zama. Gashi mu duka ‘yan gida guda zamu je jaru a ranar guda, akan laifi guda kuma. Rayuwar mu ta lallace da abinda muka kadamar”

Kakakin yada yawun jami’an tsaron yankin, Muhammad Abubakar ya bada tabbacin cewa lallai sun yadda da amince da laifin da ake zargin su da shi na kisan kai. Hukuma kuma zata dauki matakin da ya kamata a kan su da wannan.