Connect with us

Labaran Najeriya

Majalisar Dattijai na ganawa da shugaban Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya akan lamarin tsaro

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Talata, 7 ga Watan Mayu 2019, Shugaban Hukumar Jami’an Tsaron kasar Najeriya, IGP Mohammed Adamu na ganawa da Majalisar Dattijan Najeriya.

Naija News Hausa ta gane da cewa wannan zaman an gabatar da shi ne don bincike da neman hanyar magance matsalar kaseh-kashe, sace-sace da ire-iren ta’addancin da ke faruwa a kasar Najeriya.

Zaman ta halarci bayyanar mai bada shawarwari ga shugaban kasa ga lamarin gidan Majalisar Dattijai, Ita Enang hade da wasu jami’an tsaro.

Mun ruwaito a wannan gidan labarai ta mu da cewa Majalisar Dattijai sun bukaci bayyanar IGP Adamu a gaban gidan Majalisar a ranar 25 ga Watan Afrilu 2019 da ta gabata, don bada bayani akan matakin da yake dauka ko da shirin dauka ga magance matsalar hare-haren da ake fuskanta a kasar.

Ko da shike ba cikakken bayani a halin yanzu game da tattaunawar su, amma dai shugaban gidan Majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya bayyana da cewa zaman zata kasance tattaunawar kofa kulle ne.

Karin bayanai zasu biyo baya, ka zagayo wannan shafin tamu a kullum don samun labaran Najeriya ta karshe.