Connect with us

Labaran siyasa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 7 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 7 ga Watan Mayu, 2019

1. Shugaban Hukumar UNGA ta ziyarci kasar Najeriya

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, María Garces, ta isa Nijeriya a kan ziyarar aiki.

Da ita da gayyatun ta sun samu marabta daga a ranar Litinin daga jami’an ma’aikatar harkokin waje da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya ta birnin Abuja.

2. Gwamnan Jihar Kano, Ganduje na zancen tsige dukan wakilan siyasa

Gwamna Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano ya bayyana cewa za a sami babban garwaya a shugabancin Jihar Kano.

Ya bayyana hakan ne a wata jawabi da yayi a wajen taron Masu ruwa da Tsakin Jihar. ranar Lahadi da ta gabata, inda ya fada da cewa, garwaye da tsitsigewar zai shafi dukan ‘yan Siyasan Jihar amma ba da mataimakinsa, Dr Nasiru Gawuna ba.

3. ‘Yan Siyasa sun yi kokarin sa in kadamar da halin cin hanci da rashawa – Jagoran Hidimar Zaben Jihar Kwara

‘Yan Watanni kadan bayan hidimar zaben 2019, Mallam Garba Madami, Kwamishinan Hidimar Zaben Jihar Kwara, a ranar Litinin, ya yi magana game da yadda ya yi murabus da amince da cin hanci da ‘yan siyasa suka yi kokarin bayarwa a lokacin.

Madami ya gabatar ne da hakan ga manema labarai a wajen hidimar bikin Auren ‘yarsa a Minna.

4. Sojojin Najeriya Sun Dakatar da Aikin Kabu-Kabu a Jihohi bakwai

Rundunar sojojin Najeriya a ranar Lahadin da ta gabata ta sanar da dakatar da masu aikin Kabu-Kabu daga wasu yankuna a wasu jihohin arewa maso yamma ta kasar Najeriya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Sojojin sun bayyana cewa an gabatar da dokar ne don magance da kawo karshen tashin hankali, sace-sacen mutane da sauran mugayaen ayyukan da ake aiwatarwa a Arewacin kasar.

5. Gwamnatin Jihar Sokoto zata kashe Miliyan N380 don ciyar da mutane ga Azumin Ramadan

Gwamnatin Jihar Sokoto ta riga ta sanya Naira Miliyan Dari Ukku da Tamanin (N380) ga hidimar Azumin Ramadan ta shekarar 2019.

Gwamna Aminu Tambuwal ya bayyana wannan shirin ne a ranar Lahadi da yamma a Sokoto, da cewa zasu kashe wannan kudaden ne wajen ciyar da Al’ummar Jihar a lokacin Ramadan.

6. ‘Yan Hari da Makami sun Sace Kanuwar Rajistra na Makarantar Jami’a a Jihar Filatu

Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa wasu ‘yan hari da makami sun hari Makarantar Jami’an Fasaha ta Filatu (Plateau Polytechnic) da ke a yankin Heipang ta karamar hukumar Barkin Ladi.

Abin ya faru ne da Saifyar ranar Litini da ta gabata, inda Maharan suka sace wata ‘yar macce da aka gane da zama kanuwar Mista Ezekiel Rangs, Rajistra na Makarantan Jami’an Fasaha ta Filatu.

7. Hukumar Tsaron Jihar Osun sun kame Sanata Adeleke

Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan Jihar Osun sun kame dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Osun daga Jam’iyyar PDP a zaben 2019, Sanata Ademola Adeleke.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa ta ranar Litini, da cewa Adeleke ya ziyarci Ofishin Jami’an tsaron bisa kira da aka yi masa, daga nan kuma aka kame shi.

8. Kungiyar Ohanaeze sun zargi Gwamnonin Jihohi da karfafa Ta’addanci a kasar

Wata Kungiyar Iyamirai ta Najeriya da aka fi sani da Ohanaeze Ndigbo, a ranar Litini da ta wuce sun gabatar da zargin Gwamnonin Jihohin kasar Najeriya da bada hadin kai ga matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

Mista Chuks Ibegbu, Mataimaki ga Sakataren Sadarwa ta Tarayya, ya bayyana da cewa matsalar tsaro da rashin aiki da ake fuskatan a kasar Najeriya sakamakon rashin kulawa da kuma yin abin da ya dace ne daga Gwamnonin Jiha.

Ka samu kari da cikakkun labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com