#Ramadan: Kalli Abubuwan da ya Kamata kowani Musulmi ya Kaurace wa a Lokacin Ramadan

Yau ya kama rana ta biyu da fara hidimar Azumin Ramadan ta shekarar 2019. Gidan labaran nan tamu sa ruwaito a baya da Ire-Iren ‘Ya’yan Itacen Marmari da za a iya bude baki da su, da kuma amfanin su a jikin dan Adam.

A yau kuma mun gane da cewa ya dace mu kara tunar da kuma gabatar maku da abubuwa masu muhimmi da Addinin Musulunci bata amince da su ba a lokacin hidimar Azumin Ramadan.

Idan kai ko ke Musulma ne ko Musulmin kwarai, ya kamata ka kaurace wa wadannan abubawa da zai iya sa ka zunubi da kuma karya azumin ka.

  • Yin Jima’i tsakanin Ma’aurata da tsakar rana

A yayin da ba a bude baki ba, bai dace da Mace da Namiji, Ma’aurata su sadu da juna ba, musamman da rana tsaka kamin lokacin shanruwa, amma dai an halasta yin hakan da dare bayan an bude baki.

Kaurace wa wannan gargadin na iya sa ka karya azumin ka a lokacin da bai dace ba.

  • Yasashshen Magana

Naija News Hausa akwai wasu da suka saba da zaman tasha, ko zaman canba, zama irin wuraren nan kan iya jawo yasashshen kalamai.

Ka kaurace wa duk wata zance da ba zai amfanar da mutum ko mai sauraronsa ba, bai kamata aji yana fita daga bakin wanda ke cikin Azumi ba. Abin da ya dace ga mai yin Azumi shine ya kasance da yawaita ambaton Allah da karatun Qur’ani a kowane lokaci.

  • Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi, kamar su Sigari ko Giya

Kayan maye bai dace ga Musulmi ba, ko da babu Azumi. Idan ma kana hakan ne akwai bukatar cewa ka gujewa hakan, ka kaurace daga duk wasu kayan maye a yayin da ake cikin wannan azumin watan Ramadan don kauce ma illata rayuwarka.

  • Lallaci da Zina (Kallon Hotuna masu Tsiranci ko fina finan batsa)

Kalle kallen duk wani abinda zai tayar da sha’awa ko aikata zina bai dace ga mai yin azumi ba, kaurace wa wanann sharadi na iya sa mai yin azumi ya fada ga jaraba. Abin sani; idan har mai azumi ya fitar da maniyyi sakamakon ire iren wannan kalle kalle ko ma zinar kanta, tabbas Azumi ya karye, sai mutum yayi kaffara bayan watan Ramadana.

  • Yawan barci

Akwai bukata ga kowane Musulmi a lokacin watan Ramadan da kasance da yin amfani da lokacin sa wajen aikin bauta da duk wata ibadar da zata kusantar da shi ko ita ga Allah, domin samun lada da kyakkyawar makoma, don haka ake kira ga mai azumi ya kiyayi yawan barci kamar kasa da nuna lalaci.