Connect with us

Labaran Najeriya

Ramuwar Jikin IG Adamu ya nuna da cewa yana Aiki Tukuru – inji Buhari

Published

on

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana ramuwar Shugaban Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan Najeriya a matsayin alamar cewa yana aiki kwarai da gaske.

“Akwai alamun cewa IGP Mohammed Abubakar Adamu na aiki tukuru don magance matsalar rashin tsaro a kasar Najeriya, musunman ma ya rame a nauyin jikinsa” inji Shugaba Buhari.

Shugaba Muhammadu ya gabatar ne da hakan a wata ganawa da manema labarai, a ranar Lahadi da ya gabata bayan dawowan sa daga ziyarar kai tsaye da ya kai na tsawon kwana goma a kasar Turai.

Buhari ya fadi hakan ne a cikin wata bidiyo da wani dan gidan jaridan VOA, Saleh Shehu Ashaka, ya rabar a hanyar sadarwa ta yanar gizon nishadin Twitter @AshakaSaleh, inda manema labarai suka tambayi shugaba Muhammadu Buhari ko akwai watan matakin musanman akan matsalar tsaro a kasar. Sai shugaban kuma ya mayar da martani ga hakan.

“Shin za mu iya ganin wata hanya ko mataki daban da Gwamnatin Tarayya zata dauka wajen yaki da rashin tsaro, musamman ma sace-sace da ta’addanci da shine babban matsala a kasar Najeriya?”

Shugaban ya kuma amsa da cewa “Ka sani, na gane da cewa IG ya rasa nauyin jikin sa ga ramuwa; don haka, ina da tabbaci da tsammanin cewa lallai yana aiki tukuru.”

Kalli bayanin shugaba Buhari a wannan bidiyon;