Connect with us

Labaran Najeriya

PDP: Karyane, Lafiya na Kalau, Ba na kame da wata ciwon Zucciya – inji Peter Obi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mista Peter Obi, Mataimakin Atiku Abubakar, dan takaran kujeran shugaban kasan Najeriya ga zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, ya yi watsi da jita-jitan da ya mamaye layin yanar gizo da cewar yana kame da cutar zuciya.

Obi karyata wanan zancen ne a wata sanarwa da aka bayar ranar Talata, 7 ga watan Mayu da ya wuce daga bakin mai yada yawun sa, Mista Valentine Obienyem.

Naija News Hausa ta gane da cewa zancen cewa tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi na kame da Cutar Ciwon Zuciya ya mamaye ko ta ina a layin yanar gizo cikin makon da ta wuce har ga wannan makon.

Jita jitan ya bayyana da cewa Peter Obi na kwance a wata Asibitin garin Anambra, inda ake nuna masa kulawa ga cutar Ciwon Zuciya da yake dauke da ita. Harma an gabatar da cewa ana shirin kai Obi a kasar waje don bashi kulawa ta musanman idan har bai nuna alamar samun sauki ba a nan Najeriya.

Ganin hakan ne Kakakin Yada yawun Obi, Mista Obienyem ya sanar a wata gabatarwa ta ranar Talata da cewa zance ba gaskiya ba ne.

“Karya ne, Ba abin da ya samu Peter Obi, karya wadanda suka wallafa hakan ke yi.” inji shi.

“Na gane da cewa wani mara fatan Alkairi ya sanar da cewa Obi na kwance a Asibiti sakamakon ciwon zuciya. Duk mai shiri da kadamar da irin wannan karyan ba mutumin kwarai bane, kuma da alamun bai fatan ganin Peter Obi da rai. Amma da yardan Allah zasu gane da cewa Allah ne kawai ke rike da rayuwan dan Adam” inji Valentine.

KARANTA WANNAN KUMA: Kuyi Addu’a don Ci Gaban Kasar Najeriya – gargadin Shugaba Buhari ga Ramadani