Connect with us

Uncategorized

Hukumar Civil Defence sun kame wani Barawon Babur a Jihar Neja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoto kamar yadda manema labarai suka bayar da cewa Hukumar Tsaron da Kare Yancin Al’umma (NSCDC) da aka fi sani da suna ‘Civil Defence’ ta Jihar Neja sun kame wani matashi mai suna Bala Saidu, daga garin Kuta ta karamar hukumar Shiroro, da zargin sace wata babur.

An bayyana ne da cewa Saidu, mai shekaru 25 da haifuwa ya sace Babur din wani mutumi da ake kira Alhaji Uba tun daga watan Janairu da ta gabata a shekarar 2019.

Kwamandan Hukumar Civil Defence na Jihar, Mista Philip Ayuba ya bada tabbacin kame barawon, Bala Saidu, a ranar Talata da ta gabata a wata ganawa da manema labarai.

Mista Philip Ayuba ya bayyana da cewa hukumar su ta ci karo ne da Saidu a shiyar Kuta inda suka samu kwace babur da ya sace, ya kuma ci gaba da cewa Hukumar bayar da shi ga Kotun kara don daukan mataki akai.