Connect with us

Uncategorized

Rawa ta Canza! Liverpool sun lashe Barcelona da Gwalagwalai 4 – 0

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da nasarar Barcelona ga Liverpool a ganawar wasan su ta karon farko ga wasan Semi-Final ta Champions League, inda Barcelona ta lashe wasan da Gwalagwalai 3 – 0.

Kungiyar wasan Kwallon kafa biyun, watau Liverpool da Barcelona sun gana a karo ta biyu da wasan Semi-Final ta Champions League na shekarar 2019 a ranar jiya, Talata, 7 ga watan Mayu, inda wasan ta dauki zafi da barin Barcelona da waden baki.

Rawa ta Canza wa Barcelona a wasan, a yayin da ‘yan kungiyar Liverpool suka nuna zafin nama da kuzari na ganin cewa sun tsige Barcelona daga shiga kafar wasan Champions League ta karshe.

Abin ya zama da mamaki ga ‘yan Barcelona a yayin da dan kwallon Liverpool, Divock Origi ya lashe ragan Barcelona cikin minti 7 ta farkon wasan da gwal. Origi ya karasa da nuna mazantaka da taken sa na ganin cewa ya sake lasar ragar Barca da wata gwal a shafin wasar ta biyu.

Bayan hakan ne Georginio Wijnaldum, shima ya jefa nasa gwalagwalai biyu cikin ‘yan lokatai wanda ya kai Liverpool ga kirgan wasa 4 sama da 3 ga wasan.

Abin takaici ne ga Shahararren dan wasan kwallon duniya, Lionel Messi da ganin cewa Liverpool sun tsige su daga shiga wasan karshe ta Champions League ta bana. Haka Kazalika Suarez, dan wasan Liverpool na da da ya koma ga Barcelona.

Nasarar Liverpool bisa Barcelona ya zan da mamaki a yayin da mutane ke dibin cewa Mohamed Salah da Roberto Firmino basu samu daman shiga wasar ba saboda rauni da suka samu a wasan su ta baya, amma sai ga shi, sauran ‘yan wasan Liverpool sun nuna mazantaka da zafin jiki, harma da kwarewa.

A halin yanzu Liverpool jira ta ke ‘yan wasan Kwallon Ajax da Tottenham su gana a wasar su ta yau, don gane ko da wa zasu hade a wasan karshe da za a yi a ranar 1 ga watan Yuli ta shekarar 2019.