Uncategorized
Assha! Dara ta ci Gida, Injimin Wutan Lantarki da ke baiwa Abuja wuta ya rushe
Hukumar Samar da Wutan Lantarki ta Yankin Birnin Tarayyar Najeriya (AEDC) Abuja zata fuskanci duhu kan rashin wutan lantarki, hade da Jihohin da ke hade da ita, a yayin da Injimin Samar da Wutan Lantarkin yankunan ya rushe.
Naija News Hausa ta fahimta kamar yada aka sanar da cewa Na’urar da ke samar da wuta ga Hukumar AEDC ta rushe da safiyar yau Laraba, 9 ga watan Mayu a missalin karfe biyar (5am).
Hukumar AEDC ta sanar da hakan ne daga bakin babban Manajan Sadarwa, Mista Oyebode Fadipe, a wata ganawa da kungiyar manema labaran Najeriya (NAN), a yau cikin Abuja, babban birnin Tarayya.
“Wannan rushewar Na’urar zai sa matsalar rashin wutan lantarki ya shafi Jihar Kogi, Nasarawa, Niger da birnin Tarayyar kasar Najeriya (FCT)” inji Mista Fadipe.
”Muna zato da diban watakila a samu cin nasara da gyara na’urar, ganin irin kokari da gwagwarmayan da Ma’aikatan hukumar ke yi don gyara injimin.”
Ko da shike ba a bayyana sanadiyar rushewar injimin ba ga manema labarai, amma Manajan Harkokin Al’umma, TCN Malama Ndidi Mbah, ta bayyana ga manema labaran NAN da cewa zasu sanar a baya da sanadiyar rushewar na’urar.
Naija News Hausa na da sanin cewa karo ta Ukku kenan da injimin ke rushewa, ta rushe sau biyu a watan Afrilu da ta gabata.