Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 9 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 9 ga Watan Mayu, 2019
1. Kotu ta gabatar da ranar karshe karar Sanata Adeleke
Kotun Koli ta Abuja, babban birnin Tarayyar kasar Najeriya ta gabatar da ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu don karshe karar zargi da ake ga Adeleke akan hidimar zaben Jihar Osun.
Naija News Hausa ta gane da hakan ne a wata sanarwa da aka bayar ranar Laraba da ta gabata.
2. Kotun Karar zabe ta fara kadamar da bincike akan karar Atiku ga Buhari kan zaben 2019
Kotun Karar Zaben Kasa ta birnin Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya, ta kafa kai ga fara gabatar da karar da ake kan sakamakon zaben 2019 da aka kamala a watan Fabrairun.
Kotun Karar, a jagorancin Shugaban Kotun Karar, Alkali Zainab Bulkachuwa, ta koma ga zancen karar a ranar Laraba da ta wuce a missalin karfe goma na safiya.
3. Gidan Majalisar Jihar Kano ta kafa dokar Biyan Fensho ga Kakakin Gidan Majalisa da Mataimakin sa
An gabatar a Jihar Kano a ranar Talata da ta gabata da dokar biyan kudin Fensho ga Kakakin Yada Yawun Gidan Majalisar Jihar Kano da Mataimakin sa.
An gabatar ne da dokar a ranar Talata a wata zama da gidan Majalisar ta yi.
4. Kungiyar Ma’aikatan Najeriya sun Katange Gidan Mista Chris Ngige
Mambobin Kungiyar Ma’aikatan Kasar Najeriya (NLC) hari gidan Ministan Aikace-aikacen Najeriya, Dakta Chris Ngige, sun Katange gidansa da ke a shiyar Asokoro, nan Abuja.
Naija News Hausa ta gane cewa kungiyar sun yi hakan ne da safiyar ranar Laraba ta da wuce a missalin karfe biyar na safiya, akan zargin cewa Ministan yayi watsi da gabatar da hukumar NSITF da kuma sanya Kokori a matsayin Ciyaman na Kungiyar.
5. Shugab Buhari ya Kafa wata Hukuma a Arewa Maso Gabashin kasar Najeriya
A ranar Laraba da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa wata Hukumar Kadamarwa ga Arewa Maso Gabashin Kasar Najeriya (NEDC).
Naija News ta gane da cewa Shugaba Buhari yayi hakan ne kamin ganawa da Kungiyar Manyan Masu Ruwa da Tsakin kasar Najeriya.
6. APC/PDP: Kotun Kara tayi Zaman Farko kan Karar Buhari da Atiku
Kotun Kara da ke jagorancin karar hidimar zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 tayi zaman farko kan karar a ranar Laraba ta da wuce.
Kotun ta gabatar da ranar 15 zuwa ranar 16 ga Watan Mayu, 2019 don karshe karar sakamakon zaben 2019 da Atiku Abubakar ya gabatar a gaban Kotun.
7. Rikici ta Barke a Gidan Majalisar Jihar Jigawa
Gidan Majalisar Wakilai ta Jihar Jigawa sun hallaka Tambarin Iko da ake amfani da shi a Gidan Majalisar wajen kafa doka ko nuna alamar amincewa.
Naija News ta samu fahimtar cewa hakan ya faru ne a lokacin da Kakakin yada yawun ‘yan Majalisar, Alhaji Isa Idris, ya gabatar da sake wallafa wata dokar da Majalisar ke amfani da ita.
8. Liverpool zata gana da Tottenham a wasar karshe ta Champions League
Bayan Gwagwarmay da nuna kwarewa a fagen wasan kwallon kafa ta Champions League, Kungiyar Kwallon kafan Liverpool da ta Tottenham ne suka ci nasara da isa ga shafin wasan karshe.
Naija News Hausa ta kai ga gane hakan ne bayan nasarar da Kungiyar Kwallon Tottenham ta yi ga Ajax a ranar Laraba da ta wuce. Wannan ya biyo baya ne bayan nasarar Liverpool ga Barcelona a ranar Talata da ta gabata.
Ka samu kari da Cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com