Connect with us

Uncategorized

Sojojin Najeriya sun Katange rukunin ‘Yan Ta’adda a Kaduna, sun kuma Kashe Mutum Biyu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoto kamar yadda rundunar Sojojin Najeriya da ke Jihar Kaduna suka bayar, da cewa sun ci nasara da kashe ‘yan ta’adda biyu da kuma karbe makaman su a rukunin ‘yan ta’addan da ke a Gonan Bature, ta yankin Rijana da Gonar Ajiyar Hatsin Kasarami da ke a karamar hukumar Chikun.

Kakakin Yada yawun hukumar Sojojin, Col. Sagir Musa, ya bada tabbacin hakan ga manema labarai a wata sako da ya aika, cewa sun gane da ‘yan ta’addan ne a wata gonar ajiyar hatsin Kasarami da aka yi watsi da shi, da ‘yan ta’addan suka mayar da shi a matsayin wajen kwancin su da kuma inda suke boye wadanda suka sace daga cikin gari, inji Sagir.

Rundunar Sojojin sun gano da miyagun Makamai kamar su, AK 47, AK 47 magazines, da wasu mugan mahadin arsasun bindige hade da wayar Salula ta Tecno biyu.

Mista Sagir ya gargadi Al’ummar Najeriya, musanman a yankunan da ta’addanci ke yawaita da sanar da duk wata alamu da suka iya gane da su da zai taimaka ga nasarar Sojoji ga Ta’addanci a kasar.