Uncategorized
An Kashe wani Jigon Jam’iyyar APC a Jihar Rivers
Jam’iyyar shugabancin kasa, APC ta Jihar Rivers tayi babban rashi a yayin da wasu mahara da bindiga da ba a san dasu ba suka kashe wani jigon jam’iyyar, mai suna, Omunakwe Benson.
Bisa bayanin da aka bayar ga Naija News Hausa, an kashe Omunakwe ne a ranar Laraba da ta gabata a shiyar Agip Estate, da ke a Port Harcourt, babban birnin Tarayyar Jihar Rivers.
An bayyana ne da cewa ‘yan hari da makamin sun shiga gidan da Mista Benson yake ne missalin karfe 8:45 na daren ranar Laraba, a cikin wata Mota, suka kuma kashe shi.
Naija News Hausa na da sanin cewa Omunakwe Benson tsohon dan takaran kujerar Gidan Majalisar Wakilai ne a karkashin Jam’iyyar APC ta Jihar Rivers.
Wani dan uwa ga Mamaicin, Okechukwu Benson, ya bayar ga manema labarai da cewa shi yana cikin kallon wasan kwallon kafa ne a yayin da ya karbi kirar gaugawa, cewa an kashe dan uwansa.
“Na karbi kira ne a missalin karfe 9 na dare da cewa ‘yan hari da makami sun kashe dan uwa na a gidan kwancin sa. Benson bai da jayayya da wani da zai kai ga kisansa.” inji Okechukwu, a bayanin shi da manema labarai.
Okechukwu yayi kira ga Jami’an Tsaro da yin kokarin bincike da kuma gane wa’yanda suka aikata kisan dan uwansa.
Ko da shike, Kakakin yada yawun Jami’an tsaron yankin, Nnamdi Omoni, ya bada tabbacin hakan, ya kuma bayyana da cewa a halin yanzu, jami’an tsaron su sun samu kame mutane biyu da ake zargi da hadin kan kisan Mista Benson.